Likitoci 199 Cikin 280 a Jihar Zamfara Ma’aikatan Bogi Ne, Inji Gwamna Matawalle

Likitoci 199 Cikin 280 a Jihar Zamfara Ma’aikatan Bogi Ne, Inji Gwamna Matawalle

  • Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana adadin likitocin da ke aiki a jiharsa da kuma na bogi da ke karbar albashin gwamnati
  • Gwamnan ya bayyana dalilin da yasa gwamnatinsa ta jinkirta albashin ma'aikatan lafiya a kwanan nan
  • Ana yawan samun ma'aikatan bogi a Najeriya da ke karbar kudin gwamnati da sunan albashi ba bisa ka'ida ba

Muradun, jihar Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta gano likitoci 199 da ke kan tsarin biyan gwamnati alhali na bogi ne.

Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar na biyan albashi ga likitoci 280 amma a zahiri akwai likitoci 81 ne a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Matawalle ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema a gidansa da ke Maradun, hedkwatar karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi Yayin Da Najeriya Da Ukraine Ke Shirin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Ta Noma

Gwamna Matawalle ya fadi adadin likitocin bogi da na gaske a jiharsa
Likitoci 199 Cikin 280 a Jihar Zamfara Ma’aikatan Bogi Ne, Inji Gwamna Matawalle | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ya kuma kara da cewa, wannan lamari na ma'aikatan kwata-kwata babu su amma suna cin gajiyar kudi na ba gwamnati wahala wajen biyan albashi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za mu zakulo ma'aikatan bogi

Ya kuma bayyana cewa, ya gama kai da kungiyar kwadago ta NLC da sauran masu ruwa da tsaki don zakulo ma'aikatan bogin da suka dade suna lashe kudin jihar.

A cewarsa, zai yi hakan ne domin tabbatar da gyara a fannin aikin da kuma tabbatar da hukunta wadanda ke cin haram, Osun Defender ta tattaro.

A kalamansa:

"Masu ruwa da tsaki sun tabbatar min cewa abin da yasa ake samun jinkirin biyan ma'aikatan lafiya albashi yana faruwa ne saboda suna son tabbatar da abubuwa sun tafi daidai kuma muna kokarin magance duk wata kitimurmura da ke fannin lafiya nan kusa."

An kori ma'aikatan gwamnatin Kano 4 daga aiki saboda takardun bogi

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

A jihar Kano kuwa, amfani da takardun bogi ya jawo wasu mutum sun rasa aiki, an kore su gaba daya tare da daukar matakin da ya dace.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da aka yiwa wasu ma'aikatan gwamnatin jihar sama da 100 karin girma a aikin da suke yi na tsawon lokaci.

Ba sabon abu bane samun badakala a aikin gwamnati a Najeriya, ana yawan samun ma'aikatan bogi da ke karbar kudi ba tare da bin ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel