Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Wata Mata Mai Juna Biyu da Wasu Mutane Uku a Anambra

Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Wata Mata Mai Juna Biyu da Wasu Mutane Uku a Anambra

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki wani yankin jihar Anambra, sun sheke mutane hudu
  • An ruwaito cewa, an kashe mata mai juna biyu ne da wasu mutum uku maza a lokacin da aka kawo harin
  • Rundunar 'yan sandan jiahr ta tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari, ana kokarin daukar mataki

Ihiala, jihar Anambra - Mutum hudu, har da wata mata mai juna biyu sun rasa rayukansu a ranar Talata yayin da wasu tsagerun 'yan bindiga suka mamaye yankin Eziani da ke karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra a Kudu maso Gabas.

'Yan bindigan sun fara farmakin ne da misalin karfe 1 na daren jiya, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaidawa Premium Times.

Yadda 'yan bindiga suka kashe mata mai juna biyu a jihar Anambra
Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Wata Mata Mai Juna Biyu da Wasu Mutane Uku a Anambra | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An kuma bayyana cewa, 'yan bindigan sun yi harbin kan mai uwa da wabi a lokacin da suka kawo hari kan mazaunan.

Kara karanta wannan

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Yankunan Birnin Gwari, Sun Halaka Jami’an Tsaro

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, Tochukwu Ikenga a ranar Talata 10 ga watan Janairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

DSP Ikenga ya bayyana cewa, an tura jami'an 'yan sanda inda lamarin ya faru, kuma sun kwaso gawarwakin wadanda aka hallakan.

Wadanda lamarin ya rutsa dasu sun hada maza uku da kuma wata mata, kamar yadda kakakin ya bayyana, The Informant ta ruwaito.

Sai dai, bai tabbatar ko matar na dauke da juna biyu ba kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Hari na karuwa a kasar nan

Kamar dai sauran jihohin Kudu maso Gabas, jihar Anambra na ci gaba da fuskantar hare-hare a kwanakin nan daga 'yan bindiga.

Mafi akasarin hare-haren da ake kaiwa a jihar ana yinsu ne kan ofisoshin gwamnati da kuma kan jami'anta.

Kara karanta wannan

'Yan Sandan Anambra Sun Kama Matashi Kan Fada, Ya Mutu a Hannunsu

Na baya-bayan nan shine wanda ya faru makwanni biyu da suka gabata, inda 'yan bindiga suka bankawa ofishin 'yan sanda wuta.

Matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa, ya karbi kudin fansa

Wani matashi kuma a wata jihar a Kudu ya yi garkuwa da mahaifinsa, inda ya karbi kudin fansa har N2.5m.

An kama matashin ne bayan da ya karbi kudin, 'yan sanda sun bayyana irin aikin da suka yi har suka kai ga kama shi.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da bincike don tabbatar da kamo wadanda suka hada baki tare suka aikata mummunan aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel