Da Ya Ya Yi Garkuwa da Mahaifinsa, Ya Karbi Kudin Fansa Har N2.5m

Da Ya Ya Yi Garkuwa da Mahaifinsa, Ya Karbi Kudin Fansa Har N2.5m

  • 'Yan sanda sun yi nasarar kame wani mutumin da ya yi tsaurin ido ya yi awon gaba da mahaifinsa don karbar kudin fansa
  • An ce ya hada baki ne da wasu mutum biyu, inda ya tabbatar da sace uban nasa tare da neman dangi su ba da fansa
  • Bayan shan matsa, ya bayyanawa rundunar 'yan sanda shi ya aikata laifin, ana ci gaba da bincike a akai yanzu

Kambi, jihar Kwara - Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta yi nasarar kame wani matashi mai suna Issa Naigheti bisa zargin yin garkuwa da mahaifinsa tare da karbar kudin fansa N2.5m.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi da ya bayyana hakan ya ce, an kama matashin ne a yankin Kambi na Ilorin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Kama Amina Guguwa Yar Shekara 50 Kan Kashe Kishiyarta Yayin Dambe A Bauchi

Ya kuma bayyana cewa, tawagar yaki da masu garkuwa da mutane ce a jihar Kwara ta yi nasarar kame mutumin a lokacin da take aikin kakkabe masu garkuwa da mutane a jihar.

Tashin hankali yayin da da ya sace ubansa, ya nemi kudin fansa
Dan Ya Ya Yi Garkuwa da Mahaifinsa, Ya Karbi Kudin Fansa Har N2.5m | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya kuma kara da cewa, ana yin duk mai yiwuwa don ganin an kamo wadanda suka aikata laifin tare dan mutumin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya amsa laifinsa da kansa

A cewar Okasanmi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa bayan an titsiye shi inda yace ya hada baki da wasu mutum biyu don sace mahaifin nasa, Bature Naigboho a yankin Igboho/Igbeti na jihar Oyo

Hakazalika, ya amsa karbar kudin fansa daga mahaifin nasa da suka kai Naira miliyan 2.5, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, za a mayar da bincike kan wannan laifi zuwa sashen manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, inda aka aikata laifin.

Kara karanta wannan

Hunturu: NiMet ta ce za a yi tsananin hazo na kwana 3, ta fadi jihohin da hakan zai shafa

Jami'i ya yi mutuwar kasko da 'yan bindiga a Nasarawa

A wani labarin kuma, wani sufeton 'yan sanda ya mutu yayin da ya yi musayar wuta da 'yan bindiga a wani yankin jihar Nasarawa.

Hakazalika, an ce 'yan bindiga biyu sun mutu yayin da jami'an tsaron suka yi kaca-kaca da su tare da jikkata wasu da yawa.

Ya zuwa yanzu dai an adana gawar jami'in a asibiti yayin da aka jibge gawarwarkin 'yan ta'addan kuma a wani ofishin 'yan sanda da ke jihar ta Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel