'Yan Bindiga Sun Farmaki Yankunan Kaduna, Sun Halaka Jami'an Tsaro

'Yan Bindiga Sun Farmaki Yankunan Kaduna, Sun Halaka Jami'an Tsaro

  • A wani hari da 'yan bindiga suka kai yankuna biyu na karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna, 'yan bindiga sun halaka jami'an tsaro da dama a yankin
  • Rikicin ya samo asali ne, bayan jami'an tsaro sun kashe wani yaro makwanni uku da suka shude, wanda yake kulawa 'yan bindigan shanunsu
  • Hakan ne yada hatsabiban, har suka dauki fansa a jiya Litinin kan yankunan da mummunan lamarin ya auku na Kubau da Anguwan Zakara

Kaduna - 'Yan bindiga sun salwantar da rayukan jami'an tsaro da dama a yankuna biyu da suka saba cin karensu ba babbaka na karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Taswirar Kaduna
'Yan Bindiga Sun Farmaki Yankunan Kaduna, Sun Halaka Jami'an Tsaro. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Daga cikin jami'an tsaron da suka rayukansu sun hada da; jami’an NSCDC, 'yan sanda, soji da kuma wasu 'yan sa kai a ranar Lahadi, kamar yadda majiyar ta bayyana.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Arewa

"Ba ranar Lahadi bane suka fara harin, sai dai sun fara ne kwanaki hudu da suka wuce. An kai hari titin Funtua zuwa Birnin Gwari, inda jami'an tsaro da dama suka rasa rayukansu. Amma na ranar Lahadi, 'yan sa kai biyu, 'dan sanda daya da wani soja sun rasa rayukansu."

- A cewar majiyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yankunan da lamarin ya auku sune Kubau da Anguwan Zakara.

An gano yadda mummunan lamarin ya samo asali yayin da jami'an tsaro suka halaka wani yaro dake kiwon shanun 'yan bindiga.

Bayan fusata da faruwar lamarin, 'yan ta'adda masu tarin yawa sun yi dirar mikiya matsayar jami'an tsaron da aka fi sani da titin Birnin Gwari zuwa Kakangi zuwa Randagi titin dake yammacin karamar hukumar Birnin Gwari gami da aika wasu jami'an tsaro barzahu.

Wani mazaunin yankin mai suna Abubakar Kakangi, wanda ya zanta da manema labarai, ya bayyana yadda 'yan bindiga suka yi yarjejeniya da mutanen anguwa kafin barinsu su yi noma.

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Sheka ‘Dan Bindiga, Sun Kama Yaran Turji, Kachalla da Tukur

Ya bayyana yadda 'yan bindigan suke keta kauyuka don siyar da shanun da suka sata, wanda hakan baya yi wa jami'an tsaro dadi kafin kashe yaron "dake kula musu da shanu" makwanni uku da suka shude.

A cewar Kakangi,:

"Makonni uku da suka shude, jami'an tsaro sun halaka yaron da ke kula musu da shanu. 'Yan bindigan ba su yi farin ciki da kisan yaron anguwar ba.
"Hakan yasa suka yi dirar mikiya matsayar jami'an tsaro ranar Lahadi, wajen titin Birnin Gwari zuwa Kakangi, titin Randagi na yammacin yankin Birnin Gwari.
"Harin ya faru ne misalin karfe 2:00 na rana. 'Yan bingidan sun rabu gida biyu gami da kai harin kauyuka biyu, inda suka halaka jami'an tsaro da dama duk da jami'an tsaron farin kaya, 'dan sanda, 'dan sa kai da sojoji."

Sai dai, har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton Jalige bai ce komai game da lamarin ba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

Yan bindiga sun sace babban alkalin gargajiya a Edo

A wani labari na daban, wasu miyagun ‘yan bindiga sun sace shugaban alkalan kotun gargajiya na Igueben da ke jihar Eno.

An gano cewa, sun sace ta ne yayin da ta ke hanyarta ta zuwa kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel