Buhari Ya Yi Sabuwar Nadi Mai Muhimmanci Gabanin Babban Zaben 2023

Buhari Ya Yi Sabuwar Nadi Mai Muhimmanci Gabanin Babban Zaben 2023

  • Shugaba Muhammadu Buhari yana son ganin komai ya daidaita a kasar kafin ya karewar wa'adinsa a watan Mayu
  • Ana makonni kadan kafin babban zaben shekarar 2023, Buhari ya yi nadi mai muhimmanci a hukumar tattara haraji na tarayya, FIRS
  • Watanni hudu kafin karewar wa'adinsa, shugaban na Najeriya ya nada Mr Lawal Sani Stores a kwamitin hukumar FIRS

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Mr Lawal Sani Stores a matsayin mamba a kwamitin Hukumar Tattara Haraji na Kasa, FIRS.

Wannan nadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin tarayya, Abuja, ranar 9 ga watan Janairu, ta hannun Tanko Abdullahi, mashawarci na musamman kan watsa labarai da sadarwa na ministan kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Mrs Zainab Ahmed.

Buhari
Buhari Ya Yi Sabuwar Nadi Mai Muhimmanci Gabanin Babban Zaben 2023. Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

An Tono Babban Abinda APC Ta Rasa a Arewa Wanda Zai Ja Wa Tinubu Shan Kaye a Zaben 2023

Sabon wanda aka yi wa nadin da dalilin da yasa Buhari ya nada shi

Stores zai maye gurbin Ado Danjuma ne, wanda ke wakiltan Arewa maso Yamma, kuma a baya-bayan nan aka nada shi matsayin babban direkta na Hukumar Tsaro da Buga Takardun Kudi na Kasa, Vanguard ta rahoto.

A cewar sanarwar, nadin ya zama dole ne don cike gurbin da Mr Ado ya tafi ya bari.

Bayanai game da Stores

An haifi shi ne a ranar 11 ga watan Maris na 1956 a Katsina, Jihar Katsina.

Ya yi babban diploma ta kasa (HND) a bangaren kasuwanci daga Kwalejin Kasuwanci da Fasaha ta West Bromwich da ke Ingila.

Ya kuma tafi Jami'ar Bayero ta Kano, inda ya yi karatun PGD a Management da digiri ta biyu a bangaren kasuwanci (MBA) a harkar kasuwanci da saka hannun jari.

Sabon mamban na kwamitin FIRS ya shafe akalla shekaru 30 yana aiki kuma ya kware a bangarori daban-daban da samun horaswa a bangarori daban-daban, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Shin Dagaske An Garzaya da Atiku Abubakar Asibiti Neman Lafiya? Gaskiya Ta Bayyana

An kuma ce ya halarci tarukan kara wa juna ilimi daban-daban da kwasa-kwasai a gida da waje.

Mr Stores ya kasance mamba a kwamitocin hukumomi daban-daban kamar SEC, CIS, Greenwich Trustees Limited da PenCom.

Buhari ya yi nadin mukami a ma'aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani

A wani rahoton, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yarda da nadin Hon Adepoju Adeyemi Sunday a matsayin babban shugaban aika (PMG) na Hukumar Aika Sakonni ta Najeriya (NIPOST).

Kafin nadinsa, Honarabul Sunday tsohon mamba ne na majalisar wakilai na tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel