Atiku Abubakar Ya Tafi Hutawa Ne Amma Lafiyarsa Kalau, Hadimi Ya Yi Karin Haske

Atiku Abubakar Ya Tafi Hutawa Ne Amma Lafiyarsa Kalau, Hadimi Ya Yi Karin Haske

  • Hadimin Atiku ya musanta rahoton da ke yawo cewa dan takarar shugaban kasa na PDP ba shi da lafiya an tafi da shi Asibiti
  • A 'yan kwanakin ana ta kace-nace a kafafem sada zumunta kan ina Atiku Abubakar ya shiga aka daina jin duriyarsa
  • A cewar kakakin kwamitin kamfen PDP, Atiku ya tafi hutu Dubai kuma daga can zai wuce Landan

Abuja - Mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya musanta ikirarin da wasu ke yi cewa tsohon mataimakin shugaban kasan ba shi da lafiya kuma an garzaya da shi Asibitin waje.

MIsta Paul Ibe, mai taimaka wa dan takarar ta fannin midiya, ya ce a yau Litinin ake sa ran Atiku zai dira birnin Landan na kasar Burtaniya, ya kuma karyata batun cewa ba shi da lafiya.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon shugaban Najeriya ya tattara dansa sun fece Turai saboda gudun rikicin zabe

Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar Ya Tafi Hutawa Ne Amma Lafiyarsa Kalau, Hadimi Ya Yi Karin Haske Hoto: @atiku
Asali: Facebook

A shafinsa na dandalin sada zumunta watau Tuwita, Mista Ibe, ya wallafa cewa:

"Domin share tantama, mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa (1999-2007) zai dira birnin Landan yau Litinin 9 ga watan Janairu, 2023."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya tafi Landan ne bisa gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta masa na halartar wasu taruka a ranakun Talata da kuma Laraba."

PCC-PDP ya karyata labarin

Haka nan, da yake jawabi, Daraktan kwamitin sadarwa da zabe na tawagar kamfen PDP, Chief Dele Momodu, ya roki 'yan Najeriya su shure rahoton dake zargin Atiku na fama da rashin lafiya.

A cewarsa rahoton, "Baki dayansa karya me." A wata hira da jaridar Punch ta wayar tarho, Momodu ya ce:

"Ya tafi hutawa ne, duk wanda ya san shi zai iya fada maku (Atiku) ba ya wasa da hutu. Ya tafi Dubai kuma daga nan zai wuce Landan ranar Litinin. Lokacin da ya isa Dubai ni na fara magana da shi."

Kara karanta wannan

Ina Atiku Yake? Ya Sake Zuwa Dubai Kanin Likita, Kafarsa Na Ciwo: Fani Kayode

"Rahoton wasan barkwanci ne na shekara, ta ya wanda yake cikin koshin lafiya za'a ce wai a an garzaya da shi kasar waje?"

Mai magana da yawun kwamitin kamfen PDP na kasa, Sanata Dino Melaye, ya roki 'yan Najeriya su yi watsi da rahoton na karya da wasu mashahuran makaryata suka kirkira.

"Atiku na cikin koshin lafiya 100 bisa 100, gwamnatin Birtaniya ce ta gayyaci Jagaban yan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kamar yadda suka gayyaci Tinubu da Peter Obi tun farko."

A wani labarin kuma Tsohon Ministan shugaba Buhari ya tona asirin wasu shugabannin APC dake tare da Atiku a boye

Tsohon ministan Buhari kuma mataimakin shugaban kwamitin kamfen APC na kasa, Godswill Akpabio, yace wasu jiga-jigai suna yi wa Atiku aiki a boye.

Sanatan ya ce ya san wasu shugabannin APC a jihar ta Akwa Ibom, wadanda ke fadin Sai Asiwaju da rana amma da daddare su koma Atiku da PDP.

Kara karanta wannan

Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel