Edo: 'Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Babban Alkalin Kotun Gargajiya

Edo: 'Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Babban Alkalin Kotun Gargajiya

  • Miyagun 'yan bindiga wadanda ake kyautata tsammanin masu garkuwa da mutane ne sun sace shugaban alkalan kotun gargajiya a Edo
  • An gano cewa, Precious Aigbonoga na kan hanyarta ta halartar wani zaman kotu ne yayin da 'yan bindigan suka sace ta a Igueben
  • Sai dai, shugaban NBA ya tabbatar da cewa suna tattaunawa da kwamishinan 'yan sandan jihar duk a kokarin ceto mai shari'ar

Edo - Shugaban kotun gargajiya da ke yankin Igueben, Precious Aigbonoga, an yi garkuwa da ita a safiyar Litinin a Ugoneki a kan hanyarta ta zuwa kotu da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo, jaridar Punch ta rahoto.

Taswirar Edo
Edo: 'Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Babban Alkalin Kotun Gargajiya. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, a wata takardar da sakataren kungiyar lauyoyi ta Najeriya, Festus Usiobaifo, yace NBA na aiki tare da rundunar 'yan sandan jihar Edo domin tabbatar da Aigbonoga ta samu 'yanci daga masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

2023: Ana Jiran Jin Wanda G5 Zasu Goyi Baya, Sabuwar Rigima Ta Bullo PDP a Arewacin Najeriya Kan Atiku

Takardar tace:

"Shugaban kotun gargajiya ta yankin Igueben, Precious Aigbonoga, an yi garkuwa da ita da safiyar Litinin wuraren Ugoneki kan hanyarta ta zuwa kotu a karamar hukumar Igueben ta jihar Edo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Matar auren abokin aikinmu ce Afebu Aigbonoga, 'dan takarar Etsako ta yamma a karkashin jam'iyyar PDP.
"Shugaban Lion Bar, Cif Nosa Edo-Osagie ya matukar shiga damuwa da wannan labarin kuma ya kushe shi da kakkausar murya, tare da takaicin halayyar 'yan bindigan nan da suka yi garkuwa da Precious Aigbonoga, jami'ar shari'a mai saukin kai da aiki tukuru.
“Shugaban NBA yana tattaunawa da kwamishinan 'yan sanda, Muhammad Dankwara. Da izinin Ubangiji, da girmansa za a ceto ta ba tare da an cutar da ita ba kuma za a cafke 'yan bindigan. Ameen.
"Mu saka ta a cikin addu'o'inmu don Allah."

- Takardar tace.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar, FG

Raini da rashin da'a: Yahaya Bello na tuhumar basarake kan kin zuwa tarbar Buhari

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kogi yana tuhumar basarake Abdul Rahman Ado Ibrahim, Ohinoyi na kasar Ebira da raini da rashin da'a gare shi da shugaban kasa.

Ya aike masa da wasikar tuhuma kan cewa bai je tarar Buhari ba a ziyarar kaddamar da wasu muhimman ayyukan da ya kai jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel