Ana Zanga-Zanga, ‘Yan APC Sun Tada Rigima kan Zargin Shugabanni da Satar $1.5m

Ana Zanga-Zanga, ‘Yan APC Sun Tada Rigima kan Zargin Shugabanni da Satar $1.5m

  • ‘Yan Concerned Members of Enugu State APC sun ce shugabannin APC a Enugu sun ci makudan kudi
  • Shugaban wannan kungiyar, Kwamred Adolphus Ude ya dage sai an binciki su Ugochukwu Agballah
  • Agballah da ‘dan takaran Gwamnan APC a Enugu sun karyata tuhumar da ake yi masu na lakume N1bn

Enugu - Wata kwantaciyyar rigima a APC ta tashi a sanadiyyar rashin jituwa a kan rabon alawus tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar na reshen jihar Enugu.

Vanguard ta ce wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun shiga zanga-zanga a dalilin zargin da suke yi na sulalewa da Naira biliyan 1.05.

‘Yan jam’iyyar da ke bore sun ce an ki biyansu wadannan kudi da aka ware a matsayin alawus na aikin zaben wadanda da za su shiga takara.

Kara karanta wannan

NNPP Ta Bayyana Abin da Kwankwaso Yake Yi da Ya Sha Gaban Atiku, Tinubu da Obi

Jaridar ta ce wannan rigima da ake yi za ta iya kawowa yakin neman zaben APC cikas a Enugu. A makon nan Bola Tinubu yake shirin ziyartar jihar.

An aikawa NWC takardar korafi

Wata majiya ta ce masu zanga-zangar sun aika da takardar korafi zuwa ga shugabannin APC na kasa a karkashin jagorancin Abdullahi Adamu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan APC na reshen jihar sun ce dole shugaban jam’iyya, Ugochukwu Agballah da Uche Nnaji mai neman Gwamna suyi bayanin inda kudi suka shiga.

'Yan APC
Taron magoa bayan APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Martanin wadanda ake tuhuma

Fidelis Edeh wanda shi ne Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Nwakaibie Uche Nnaji ya fadawa ‘yan jarida NWC tana bibiyar batun.

Edeh yake cewa shugabannin jam’iyya na kasa za su duba su ga ko an fitar da wadannan kudi, a cewarsa wannan ba aikin ‘dan takarar Gwamna ba ne.

Kara karanta wannan

Miyagun da Suka Yi Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa Sun Fadi Abin da Suke Bukata

Daily Post ta rahoto Ugochukwu Agballah yana musanya wannan zargi, yake cewa majalisar NWC ba ta aikowa APC ta reshen jihar Enugu da wasu kudi ba.

Ina $1.5m da aka yi tanadi? - Kungiya

Amma shugaban ‘yan Concerned Members of Enugu State APC, Kwamred Adolphus Ude ya zargi shugabanninsu da facaka da kudi da rashin sanin aiki.

A lissafin Adolphus Ude da mutanensa, akwai $1.5m (N1.050b) da aka warewa masu tun lokacin zaben tsaida ‘dan takara, amma aka hana su hakkinsu.

Jaridar Legit.ng Hausa ta tuntubi Aliyu Adam wanda shi ne sakataren jam'iyyar NNPP da ake yi wa lakabi da mai kayan marmari, na reshen Enugu.

Aliyu Adam ya shaida mana APC a wargaje ta ke a jihar Enugu, ya kuma ce ba komai ya kawo wannan ba illa rikicin kudi da sabani a kan rabon mukamai.

Tinubu zai bada mamaki - PCC

A yau aka ji labari Sanusi Garba Rikiji ya ce daga jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa, Zamfara, Sokoto da Kebbi, APC za ta samu kuri’a miliyan 5.3

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Tsohon shugaban majalisar jihar Zamfara, Rt. Hon. Rikiji sun fito da wani tsari da ake kira 30-30 a kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu a yankinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel