Ba Dan Buhari Ya Kawo Mana Agaji Ba Da Tuni Jihar Imo Ta Tarwatse. Uzodinma

Ba Dan Buhari Ya Kawo Mana Agaji Ba Da Tuni Jihar Imo Ta Tarwatse. Uzodinma

  • Gwamnan Imo ya bayyana tsabar godiyarsa ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bisa ceto jiharsa daga watsewa
  • Hope Uzodinma yace Allah da taimakon Buhari ne suka ceto Imo daga rushe wa yayin da matsalar tsaro ta taso jihar a gaba
  • Yace Ibo zasu jefa wa jam'iyyar APC kuri'u a babban zabe mai zuwa ko dan gadar Niger ta biyu da Buhari ya kammala

Imo - Gwamnan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, Hope Uzodinma, ya nuna tsantsar jin dadi da godiya bisa dumbin taimakon da jiharsa ta samu daga gwamnatin tarayya.

Gwamna Uzodinma ya bayyana cewa ba dan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba, da yanzu babu zancen jihar Imo, ta wargaje baki daya saboda ayyukan ta'addanci, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma.
Ba Dan Buhari Ya Kawo Mana Agaji Ba Da Tuni Jihar Imo Ta Tarwatse, Uzodinma Hoto: Hope Uzodinma
Asali: UGC

Uzodinma ya yi wannan furucin ne yayin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels tv a cikin shirinsu mai taken Politics Today.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Gwamna ya fadi dalili 1 da yasa gwamnonin APC a Arewa ke son Tinubu

A cewar gwamnan, jiharsa ta sha fama da matsalolin tsaro da suka hada da ayyukan ta'addancin 'yan bindiga da garkuwa da mutane, ga uwa uba matsain rayuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da jaddada cewa hanzarin gwamnatin tarayya karashin shugaba Buhari na kawo wa jihar dauki ne ya ceto Imo da ga tarwatsewa.

"Allah da kuma gwamnatin tarayya ne suka ceto jihar Imo," inji gwamna Uzodinma, mamban jam'iyyar APC mai mulki.

Shin Tinubu zai uya lashe kuri'un mutanen Imo?

Yayin da aka tambaye shi ko dan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu, zai iya kai labari a babban zabe mai zuwa, Uzodinma ya ba da amsa mai jan hankali.

Ya nuna yakinin cewa Tinubu ne zai lashe zabe, inda ya bayyana cewa ko gina babbar gadar Neja ta biyu kadai ya isa dalilin da zai ja hankalin Inyamurai su zabi APC.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

A kalamansa yace, "APC ce jam'iyyar da zata samu nasara a jihar Imo, ku ce ni na fadi haka a ko ina kuka je."

Gwamnatin Ondo ta sa dokar zaman gida

A wani labarin kuma Gwamnan APC Ya Kakaba Dokar Zaman Gida Tsawon Awa 24 a Kowace Rana Har Sai Baba Ta Gani

Gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya kakaba dokar zaman gida ta awa 24 kullum a Ikare-Akoko har sai baba ta gani.

Gwamnan ya yi haka ne sakamakon rikicin da ya barke tun shigowar sabuwar shekara kuma ya ci gaba da ruruwa a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel