Gwamna Akeredolu Ya Kakaba Dokar Zaman Gida A Yankin Jihar Ondo

Gwamna Akeredolu Ya Kakaba Dokar Zaman Gida A Yankin Jihar Ondo

  • Gwamnan Ondo ya kakaba dokar zaman gida kan mazauna garin Ikare-Akoko har sai baba ta gani
  • A wata sanarwa da gwamnatin Ondo ta fitar tace an dauki matakin ne bayan ruruwar wutar rikici tun ranar Talata
  • Rashin zaman lafiyan ya samo asali ne tun daga wurin shagalin murnar shigowar sabuwar shekara da wasu matasa suka shirya

Ondo - Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya kakaba dokar zaman gida ta tsawon awanni 24 a kowace rana a garin Ikare-Akoko, hedkwatar karamar hukumar Akoko ta arewa maso gabas.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bayan danbarwan da ta barke har da kashe-kashe a wurin shagalin shigowar sabuwar shekara.

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu.
Gwamna Akeredolu Ya Kakaba Dokar Zaman Gida A Yankin Jihar Ondo Hoto: Oluwarotimi Akeredolu
Asali: Depositphotos

An ce rashin zaman lafiya ya mamaye garin ne ranar Talata lokacin da shagalin sabuwar shekara da matasa suka shirya ya sauya salo, aka fara ruwan harsashi.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki, Ta Tona Asirin Mai Hana Ruwa Gudu a Rigingimun PDP

Rahotanni daga garin Ikare sun nuna cewa masu ba da nishaɗi a wurin da mazauna yankin sun ari na kare domin tsira da rayuwarsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar wasu majiyoyi, harin 'yan bindigan da ya wargaza shagalin ba zai rasa alaka da faɗan karfin iko tsakanin basaraken Owa-Ale da kuma Olukare na Ikare, Sarakuna biyu da ake da su a garin.

Kowa ya zauna a gida har sai baba ta gani - Gwamnatin Ondo

Kakaba dokar zaman gidan na kunshe ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Alhamis a Akure dauke da sa hannun sakataren watsa labaran gwamna, Richard Olatunde.

Sanarwan tace an dauki matakin sanya dokar ne a wurin taron tsaro na jihar Ondo karƙashin shugabancin mai girma gwamna, Punch ta ruwaito.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"An yi haka ne bayan kara tsanantar rikici wanda ya samo asali tun ranar Talata, ya ci gaba da yaɗuwa ba tare da kawo karshensa ba kuma gwamnati ta zauna a manyan Sarakuna da nufin shawo kan mutane."

Kara karanta wannan

Kaico: Tashin hankali yayin da mai siyar da fetur ya babbake abokinsa a kan cajar waya

"Muna umartan jami'an tsaro su tabbatar mutane sun bi wannan doka sau da kafa, tuni aka kaddamar da bincike domin zakulo asalin abinda ya haddasa rikicin."
"Domin dawo da zaman lafiya, gwamnati ta garkame Ikare-Akoko baki daya, ba'a son ganin motsin kowa a waje ba tare da izinin mahukunta ba har sai baba ta gani."

A wani labarin kuma Wasu Miyagu sun je har gida, sun Yi Wa Shugaban PDP Yankan Rago a Jihar Sakkwato

Bayanai sun nuna cewa da yuwuwar lamarin na da alaka da siyasa saboda jigon PDP a garin Asare ya dawo gida daga wurin kamfe kenan aka zo aka ƙashe shi.

Baya ga kisan shugaban PDP, maharan sun kuma harbe yayansa har lahira nan take yayin da ya yi yunkurin kai dauki ga dan uwansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel