Dalilin da Yasa Gwamnonin APC Na Arewa Ke Son Tinubu Ya Gaji Buhari a Zaben Bana

Dalilin da Yasa Gwamnonin APC Na Arewa Ke Son Tinubu Ya Gaji Buhari a Zaben Bana

  • Gwamnan APC a Arewacin Najeriya, Abdullahi Sule ya bayyana zaman da ake tsakanin Tinubu da gwamnonin APC na Arewa
  • An yada batun cewa, wasu gwamnoni 11 na APC na shirin marawa Atiku baya, gwamnan ya yi watsi da batun
  • Ana ci gaba da fuskantar zaben bana na 2023, 'yan siyasa na ci gaba da bayyana kalamai masu sukar juna

Lafia, jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana dalilan da suka sa gwamnonin Arewa na APC suka amince shugaban kasa na gaba ya fito daga Kudu kuma suke gangami don tallata Tinubu.

A hannu guda, gwamnan ya yi watsi da jita-jitan da ake yadawa cewa, wasu gwamonin Arewa na APC 11 suna kus-kus a wani yunkuri na marawa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar baya.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023

Sule ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa bayan da ya gana da jiga-jigan jam’iyyar APC a jiharsa gami da mambobin majalisar kamfen dinsa.

Gwamna ya fadi dalilin da yasa suke son Tinubu
Dalilin da Yasa Gwamnonin APC Na Arewa Ke Son Tinubu Ya Gaji Buhari a Zaben Bana | Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

An yi wannan ganawa ne a gidan gwamnatin Nasarawa da ke birinin Lafiya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule ya yi watsi da ikrarin cewa, babu wani shiri daga gwamnonin APC don cin amanar Tinubu ko jam’iyyar nan da babban zabe da za a yi cikin shekarar nan.

Ya kuma bayyana cewa, babu wani dalili da zai sa gwamnonin su ki goyon bayan Tinubu a zaben da ke tafe nan wata guda da kwanaki kadan.

Hakazalika, ya shaida cewa, babu wani batu a kasa daga wasu gwamnonin APC da ke kokarin hada kai da Atiku don tabbatar da ya ci zabe a 2023.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Ga Atiku, Tinubu Ya Ziyarci Fitaccen Gwamnan G5, Bidiyo da Hotuna Sun Bayyana

Daga ina wadannan batutuwa ke fitowa masu ikrarin gwamnonin APC za su marawa Atiku baya?

A cewar gwamna Sule, mutane kashi biyu ne ke yada irin wadannan maganganu, kuma ya ce sharrinsu zai kare a kansu, Whistler ta tattaro.

A kalamansa:

“Wadannan karairayi na fitowa ne galibi daga bangarori biyu na mutane. Daya dai shine ‘yan adawa da ke yin duk mai yiwuwa domin damunmu saboda babu wanda ke son Tinubu ya lashe zabe kamar gwamnonin APC na Arewa.
“Dalilin shine idan gwamnonin APC daga Arewa suka gane cewa muna son ci gaba da rike mulki daga Arewa, gwamnonin APC sun tashi da cewa a’a, kujerar ya kamata ta koma Kudu domin a mutunta mu a matsayin wadanda suka yi imani da Najeriya.
“Bayan Baba (Shugaba Muhammadu Buhai) ya yi shugabanci na shekaru takwas tare da taimakon ‘yan Kudu, idan a yau muka ce muna kuma bukatar ci gaba da rike matsayin, duniya ba za ta mutunta ‘yan Arewa ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Sanatan APC Ya Bayyana Yadda Kwankwaso Da Obi Ke Yi Wa Tinubu Aiki

“To wannan dai sgine dalilinmu tilo. Kuma ba kowa ne ke tare da mu ba amma Allah masani ne, muna da shugaban kasa mai sauraranmu kuma ya saurare mu kuma tabbas mun yi nasarar ba Tinubu matsayin."

A bangare guda, mataimakin Tinubu ya bayyana cewa, a fahimtarsa abokin takararsa lafiyarsa lau, don haka babu wata barazana game da shugabancinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel