Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022

Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022

Shekarar da ta gabata ta 2022, ta kasance daga cikin shekarun da 'yan Najeriya ba za su taba mantawa ta ita ba cikin gaggawa a rayuwarsu.

Abubuwa da yawa masu daukar hankali sun faru, kuma 'yan kasar sun yi maganganu da martani mai daukar hankali kan duk wani maudu'in da ya tashi.

A rahoton nan, mun tattaro muku kadan daga abubuwan da suka faru a 2022 da kuma yadda suka faru, da ma dai dalilin faruwarsu.

Daga cikin abubuwan da suka faru masu daukan hankali sun hada da:

1. Yajin aikin ASUU

Makwanni bakwai kacal a farkon shekarar 2022, kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta shiga yajin aiki a ranar 14 ga Fabrairu.

Yajin aikin ASUU
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kawi karshen yajin aikin a ranar 14 ga watan Oktoba, watanni takwas kenan bayan fara shi. Sama da dalibai miliyan biyu a jami'o'in gwamnati an hana su zuwa jami'oi.

Kara karanta wannan

2023: Sunaye da Gudumawar da Mutum 7 Zasu Bayar Wurin Canza Fasalin Najeriya

2. Dokar zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudurin dokar gyaran kudin zabe a watan Fabrairun 2022 bayan ya ki amincewa da shi har sau biyar – bisa dalilan da suka hada da yawan kudaden da ake kashewa a zabe, rashin tsaro, da dai sauran su.

Dokar zabe ta Buhari
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Dokar ta bai wa hukumar zabe damar sake duba abubuwa da yawa suka shafi yadda ake tafiyar da zabe da ayyukansa a kasar.

3. Harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

A ranar 28 ga watan Maris ne wasu tsageru dauke da muggan makamai da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka fito daga dajin Kateri-Rijana na jihar Kaduna, inda suka tada bama-bamai kan titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna dauke da fasinjoji 362.

Harin ya kai ga yin awon gaba da fasinjoji sama da 100. Akalla mutane takwas ne suka mutu a harin.

Yadda aka farmaki jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su sun kubuta ne bayan biyan fansa, wasu kuwa bayan tattaunawar hukumomin gwamnati da wadanda suka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Fitaccen Sarki a Arewa, Sun Tafka Ta'asa

Watanni bayan dakatar da ayyukan jirgin, an sake bude hanya, ya ci gaba da aiki a wtaan Disamba.

4. Mutuwar Alaafin na Oyo

Alaafin na Oyo na 44, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi Alowolodu III mai dogon zamani, ya rasu a ranar 22 ga Afrilu 2022.

Mutuwar Alaafin na Oyo
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Alaafin ya rasy yana da shekaru 83 kuma ya yi sarauta tsawon kusan shekaru 52, wanda shine mafi dadewa a tarihin kowane Alaafin.

5. Zaben fidda gwani na Shugaban Kasa

'Yan takara 18 ne ke takarar neman zama shugaban kasar Najeriya. Jam’iyya mai mulki ta APC ta zabi tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu a matsayin wanda zai rike mata tuta a 2022.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya samu tikitin PDP a zaben na bana.

Zaben fidda gwanin APjam'iyyu
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Peter Obi - tsohon gwamnan jihar Anambra ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, sai kuma Rabi'u Kwankwaso - tsohon gwamnan Kano da ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

6. Harin gidan yarin Kuje

Da tsakar daren 6 ga watan Yuli, ‘yan ta’adda sun kai hari gidan gyaran hali na Kuje da ke babban birnin tarayyar Najeriya tare da tada bama-bamai.

Harin ya kai ga sakin wasu kasurguman shugabannin 'yan ta'addan Boko Haram da suka addabi jama'a kuma suke tsare a magarkamar.

Kuje: Yadda aka kai har gidan yarin Abuja
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

'Yan ta'addan ISWAP da ke da alaka da ISIS sun ikirari tare da daukar alhakin kai harin.

Hakazalika, majiyoyin sirri na tsaro sun ce, akwai gamin kai tsakanin kungiyar ta ISWAP mai barna a Arewa maso Gabas da ta Ansaru da ke nata barnar a Arewa maso Yamma a wannan harin.

Kimanin fursunoni 879 ne daga cikin 994 suka tsere, sannan sama da 400, ciki har da 'yan ta'addan Boko Haram sama da 50 ake ci gaba da neman inda suka shiga.

7. Kama Abba Kyari

An kama wani fitaccen jami’in dan sanda mai suna Abba Kyari bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Hakura Ba" Gwamnan Arewa Da Aka Yi Wa Ruwan Duwatsu Ya Magantu

An zarge shi da kulla harkalla da tawagar masu safarar miyagun kwayoyi, haramtattun kayayyaki daga kasashen Brazil, Habasha da Najeriya, in ji NDLEA.

Harkallar Kyari da kwaya da kuma damfara
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Kafin badakalar miyagun kwayoyi, tuni an dakatar da Kyari bisa zarginsa da hannu a wata damfarar da Hushpuppi ya yi a kasar waje.

8. Matsalar ambaliyar ruwa

Najeriya kan fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a kowace shekara, galibi sakamakon rashin isassun magudai da sauran more rayuwa da kuma ta fannin jama'a; rashin kula da ka'idojin tsaftace muhalli.

Amma a bana, hukumomi sun dora alhakin wannan ambaliyar kan ruwa da ke kwararowa daga koguna a kasar, mamakon ruwan sama da kuma sakin ruwa da ya wuce gona da iri daga kasashen waje kamar madatsar ruwan Lagdo da ke Kamaru, mai makwabtaka da Najeriya.

An yi ambaliyar ruwa a 2022
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mummunar ambaliyar ruwa ta mamaye kauyuka da manyan birane; kuma hakan ya kai ga cinye gonaki a kusan dukkan sassan Najeriya.

Wannan dai shi ne mafi munin yanayi na sauyin yanayi da Najeriya ta fuskanta tun bayan aukuwar bala'i mai kama da wannan a 2012.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige Buhari da Tirka-Tirka 10 da Aka Yi a Majalisar Tarayya a Shekarar 2022

9. Satar mai

A mafi akasarin kwanakin 2022, an jefa ‘yan Najeriya cikin rudani sakamakon karancin mai da ake gani a fadin kasar.

A yayin da ke ci gaba da yin ta’azzara, Najeriya na ci gaba da tafka asarar kusan ganga 437,000 na man fetur, kuma kungiyoyin tada zaune tsaye da daidaikun mutane ne ke fasa bututun mai a yankin Neja Delta.

An yi satar mai a 2022
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Man da aka sace a 2022 ya kai na sama da $10bn, kwatankwacin Naira Tiriliyan 4.3 (N430 zuwa Dala).

10. Sake fasalin Naira

Yayin da 2022 ke gab da karewa, babban bankin Najeriya ya kaddamar da sabbin tsare-tsare don sake fasali da maye gurbin wasu daga cikin kudaden Najeriya.

Bankin ya ce yana da burin rage yawon kudade a hannun jama'a don rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma magance yawan jabun kudade a hannun jama'a.

An sauya fasalin Naira
Abubuwa 10 da Suka Dauki Hankalin Jama’a a Najeriya a 2022 | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Kudaden da aka sauyawa fasali sun hada da N200, N500, da N1000, kuma tuni sun fara aiki a kasar. Za a daina amfani da tsoffin kudade a ranar 31 ga Janairun bana.

Kara karanta wannan

Yadda Na Sha Bulala A Makaranta Saboda Laifi Daya Da Nake Wa Malamai, Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.