Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Oyo, Alaafin Lamidi Adeyemi

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Oyo, Alaafin Lamidi Adeyemi

Da safiyar Asabar aka samu labarin cewa Allah ya yiwa Sarkin Oyo, babbar Sarki a kasar Yarbawa, Oba Lamidi Adeyemi, rasuwa.

Oba Adeyemi ya mutu ne da yammacin Juma'a a Asibitin koyarwa jami'ar Afe Babalola dake Ado Ekiti, rahoton Premium Times.

Cikin dare aka gaggauta kai gawarsa jihar Oyo domin fara shirin jana'izarsa.

Adeyemi ya mutu yana mai shekaru 83 kuma ya yi shekaru 52 kan mulki.

Alaafin Lamidi Adeyemi
Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Oyo, Alaafin Lamidi Adeyemi Hoto: @theakinakinboye, @YourDarlinging
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayinda ake shirye-shiryen jana'izarsa, ga abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Alaafin:

1. An haifi Alaafia of Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Atanda Adeyemi III, ranar 15 ga Oktoba, 1938.

2. Ya fito daga gidan sarautar Alowolodu kuma dan gidan Oranmiyan ne

Kara karanta wannan

Sarkin Oyo ya hango mutuwarsa, ya fada mana cewa magabatansa sun yi kira - Hadimarsa

3. Mahaifinsa, Raji Adeniran, ya zama Sarkin Oyo a 1945 kuma aka tsigeshi a 1954

4. An nadashi Sarkin Oyo a ranar 18 ga Nuwamba, 1970 yana dan shekara 31 bayan mutuwar Alaafin Gbadegesin Ladigbolu II

5. Dan dambe ne kafin zama Sarki

6. Ya mutu ya bar mata 11 da ya aura, kuma babbar uwargidarsa ita ce Ayaba Abibat Adeyemi.

7. Ya yi aiki a kamfanin Royal Exchange Assurance dake Legas

8. A 1979, an karramashi da matsayin CFR a Legas

9. A 1980, shine Chansalan Jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto na farko, kuma yayi shekaru 12 kan kujerar

10. A shekarar 1975, ya yi aikin Hajjinsa na farko tare da Shugaban kasar Soja na lokacin, Janar Murtala Muhammad.

A 1990, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nadashi Amirul Hajj bisa kokarinsa wajen ganin cigaban Musulunci.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel