Cristiano Ronaldo Ya Samu Kulob da Zai Koma, Zai Iya Tashi Da €400m a Shekaru 2

Cristiano Ronaldo Ya Samu Kulob da Zai Koma, Zai Iya Tashi Da €400m a Shekaru 2

  • Kungiyar Al-Nassr ta shiga cikin masu yin zawarcin Cristiano Ronaldo wanda a halin yanzu bai da kulob
  • Idan zai buga mata kwallo na shekaru biyu da rabi, Al-Nassr za ta kashewa Ronaldo €400m nan da 2025
  • Babu tabbacin cewa ‘dan wasan mai shekara 37 ya shirya barin nahiyar Turai, ya koma kasashen Larabawa

Qatar - Rahotanni na zuwa cewa tsohon ‘dan wasan gaban Manchester United, Cristiano Ronaldo yana kan gabar komawa Al-Nassr da buga wasa.

A wani rahoto da jaridar Marca ta fitar, an ji cewa kungiyar ta Al-Nassr da ke kasar Saudi Arabiya ta ba babban ‘dan wasan kwangila na shekara biyu.

Kungiyoyin kasashen Amurka suna neman sayen ‘dan wasan idan har ya yarda ya bar Turai, ana haka ne sai Al-Nassr ta nuna sha’awar ‘dan kwallon.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Umurnin Kai Shi Kurkuku: Shugaban Yan Sanda Nigeria Yayi Martani

Kungiyar za ta biya Ronaldo €400m idan ya yarda ya buga mata wasa har zuwa shekarar 2025. A shekara idan aka yi lissafi, yana da akalla N91.2bn.

Ronaldo zai hadu da Ospina?

Jaridar Goal.com tace idan ‘dan wasan na kasar Portugal ya karbi tayin Al-Nassr, zai hadu da David Ospina wanda ya taba bugawa kungiyar Arsenal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

David Ospina shi ne mai tsaron ragar Arsenal ta kasar Ingila tsakanin shekarar 2014 zuwa 2019.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo a Ingila Hoto: @manutd
Asali: Twitter

Babu mai sayen Ronaldo a Turai?

A halin yanzu tsohon ‘dan wasan na Real Madrid da Juventus yana kasar Qatar inda ake buga gasar cin kofin Duniya, kasarsa ta isa zuwa zagaye na gaba.

Masu nazarin kwallo su na tunanin Chelsea ba ta da sha’awar sayen ‘dan wasan – Haka zalika kungiyar Newcastle da take hannun Larabawan Saudiya.

Shugaban kungiyar Bayern Munich, Oliver Kahn ya nesanta kulob dinsu da tauraron Duniyan.

Kara karanta wannan

LP Ta Batawa Atiku Lissafi, Shugaban PDP Yana Goyon Bayan a Zabi Peter Obi

Eurosport tace duk shekara, Cristiano Ronaldo zai samu £172.9m a kungiyar kwallon kafan Larabawan da tayi shekaru uku ba ta ci gasar kasar Saudi ba.

Wata hira da Ronaldo ya yi, inda aka ji ya soki Erik ten Hag da yadda ake tafiyar da Manchester United tayi sanadiyyar da kungiyar ta katse kwantigarinsa.

An yaudare ni - Ronaldo

An ji labari Cristiano Ronaldo ya soki Manchester United, ya koka kan yadda ake gudanar da abubuwa a kungiyar, yace babu wani cigaban da aka samu.

Ronaldo ya zargi kocinsa da rashin girmama shi, sannan kuma ya maidawa tsofaffin abokansa irinsu Wayne Rooney martani saboda yawan sukarsa da suke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel