Shekarar 2022 Ta Zama Wata Shekarar Tarihi Wajen Tashe-Tashen Hankula Da Rashin Tabbas

Shekarar 2022 Ta Zama Wata Shekarar Tarihi Wajen Tashe-Tashen Hankula Da Rashin Tabbas

  • A farkon wannan shekarar ne aka fara kaiwa jirgin kasan Abuja zuwa kaduna hari tare da garkuwa da fasinjojinsu.
  • A dai wannan shekarar ne akaiwa kauyen Matunji dake karamar hukumar mulki ta Maru a jihar Zamfara ruwan wuta sakamakon 'yan bindiga sun boya a kauyen
  • A wannan shekarar aka kaiwa tawagar motocin shugaban kasa hari yayin da ayarin motocin ke isa ga mahaifarsa ta Daura

Abuja - An sha fama da ambaliyar ruwa, yawan mace-mace, yajin aikin malaman jami'oi na tsawon wata takwas, satar mutane dan kudin fansa, tabarbarewar tattalin arziki na cikin abubuwan da sukaiwa shekarar 2022 katutu a NIgeria

Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta ce a shekarar 2022 akwai 'yan Nigeria kimanin Miliyan 133 da suke cikin kangin talauci baya ga yara kusan Miliyan 20 da basa zuwa makaranta, wanda hakan ke nuna fiye da rabin yan Nigeria matalauta ne kuma yaransu basu da ilimi.

Kara karanta wannan

2023: Idan Atiku Ya Hau Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Kara Kwana da Yunwa, Gwamnan PDP

Baya ga halin kunci da tatttalin arzikin kasar nan ya shiga, 'yan siyasa sun fitar da wukakensu da ga kufe muraran da kuma neman darewa ko maimaita kujerunsu ko na sama da su a babban zaben da ke tunkarar kasar nan na shekarar 2023

Wayyo Allah Talaka: Mutum 8,058 Aka Raba Da Rayuwarsu A Nigeria

Abinda yake a bayyane shine mutane kusan 8,058 da doriya ne aka kashe a Nigeria sanadiyar tashe-tashen hankula dabam-dabam wanda suka hada da garkuwa da mutane, aikin 'yan kungiyar Boko-Haram, aikin 'yan awaren IPOB da dai sauransu

Baya ga wadancan rashe-rashen da aka samu ta sanadiyar aiyukan masu kawowa kasar nan barazanar zaman lafiya, hatta hukumomin tsaron kasar nan sunyi sanadiyar rasa rayukan wasu daga cikin fareren hula a kasar sabida aiyukan na sakaci ko kuskure. Rahotan Vanguard

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kwankwaso a Gusau Jihar Zamfara: Zan Ba Da Fifiko Kan Muhimman Abubuwa 2 Idan Na Ci Zaben 2023

Ambaliyar Ruwan Sama Da 'Barnar Da Ta yi

Baya ga bala'in da aka samu na rasa rayuka, akalla ambaliyyar ruwan bana tayi sanadiyyar jikkata 'yan Nigeeria kusan mutum 2,407 baya ga wanda suka rasa gidajensu ko kuma suka rasa matsugunnansu. Gonaki da filayen noma dai duk sun salwanta dalilin ambaliyar banan.

Nigeria
Shekarar 2022 Ta Zama Wata Shekarar Tarihi Wajen Tashe-Tashen Hankula Da Rashin Tabbas Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

Tattalin Arziki

A watan oktoban wannan shekarar gwamnann babban banki CBN, ya sanar da sakewa kudin kasar nan fasali wanda yace sauya fasalin zai shafi N200, N500 da kuma N1000. wanda tuni aka sauya musu fasalin kuma aka sanar da ranar da za'a daina amfani da tsoffin kudin.

To sai dai masana sunyi ta fasshin baki kan batun sauyin inda suka nuna ba kamarin tasgaro zai kawo ga tattalin arzikin kasar ba, musamman ma a tsakanin matsakaita da matalautan kasar.

Yajin Aikin Malaman Jami'o'i

A wannan shekarar ne dai malaman jami'o'i suka tafi yajin aikin kwana 243 (sati 34) sakamakon kin biyansu hakokinsu da gwamnatin tarayya tayi, wanda sai a ranar 14 ga watan oktoban wannan shekarar malaman suka koma bakin aikinsu.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan Ya Sake Rokon 'Yan Bindiga Su Aje Makamai Gwamnatinsa Zata Yafe Masu

Sabida matsalar da gwamnatin tarayya ke samu da kungiyar,malaman jami'o'in ta fitar da ssanarwar kafa wata sabuwar kungiyar malaman mai suna CONUA da kuma kungiyar masu koyar da aikin kula da lafiyar hakori mai suna NAMDA.

Zabe

A shekarar da zamu shiga ta 2023 ake sa ran za'a gudanar da babban zaben Nigeria, inda za'a zabi shugaban kasa da 'yan majalissar dattijai dana tarayya a watan Faberu da kuma gwamnoni da 'yan majalissar jiha a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel