Gudaji Kazaure: Buhari Ya Yi Magana Kan Gaskiyar Bacewar Naira Tiriliyan 89 a Bankuna

Gudaji Kazaure: Buhari Ya Yi Magana Kan Gaskiyar Bacewar Naira Tiriliyan 89 a Bankuna

  • Mai magana da yawun bakin shugaban kasa ya ce a 2016 wasu sun yi ikirarin N20tr sun bace a bankuna
  • An ba masanan da suka yi wannan zargi aikin gano kudin da suka yi kafa, amma suka gagara yin nasara
  • Daga baya Garba Shehu ya ce aka rusa aikinsu, sai suka sake lallabowa ta bayan kwamitin Gudaji Kazaure

Abuja - Ta bakin Malam Garba Shehu, Fadar shugaban kasa ta ce ta tabbata cewa babu hujjar da ke iya nuna N89.09tr daga kudin da ake karba a bankuna.

The Cable ta rahoto Garba Shehu ya fitar da jawabi yana cewa zargin da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure yake yi na bacewar kudi, ba gaskiya ba ne.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasar ya ce da Muhammadu Buhari ya hau mulki, ya fahimci akwai matsala game da kudin da bankuna ke karba.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa: Kwamitin Gudaji Kazaure Haramtacce Ne, Ba Buhari Ne Ya Kafa Sa Ba

A lokacin an zargi jami’an hukumar NIPOST da hada-kai da bankuna wajen satar kudi. Wannan ya sa wasu masana suka yi zargin cewa N20tr sun bace.

Binciken kudi bai je ko ina ba

Hadimin shugaban kasar ya ce an samu masana da suka yi ikirarin za su gano kudin da suka yi kafa ta NIBSS, sai gwamnati ta ba su kason 7.5% na kudin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shehu yace ganin aikinsu ya gagara zuwa ko ina, sai Marigayi Abba Kyari ya rubuta takarda, ya bada umarni ayi watsi da binciken da masanan nansuke yi.

Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Jawabin ya nuna an kai gwamnati kotu a kan wannan yarjejeniya, a karshe aka ba gwamnati gaskiya. A cewarsa, tun lokacin ake yi wa gwamnati barazana.

Ta haka Hon. Kazaure ya bullo

A haka aka samu kwamitin Muhammadu Gudaji Kazaure da sunan za su gano kudin da suka bace bayan Abba Kyari ya yi watsi da wancan aiki da aka soma.

Kara karanta wannan

Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi

Ganin cewa tuwo aka yi kokarin canzawa suna, Garba Shehu ya ce shugaban Najeriya ya rusa kwamitin da aka nada Gudaji Kazaure a matsayin sakatarensa.

Tun daga lokacin da shugaban kasa ya janye amincewar da ya bada, kwamitin ya tashi aiki wanda dama tun can Shehu ya ce aikinsu ya saba tsarin mulkin kasa.

Babu N89tr a bankunan Najeriya

A karshen jawabinsa, Shehu ya ce babu hujjar da za ta nuna N89tr sun yi batan-dabo kamar yadda a 2016 wadannan masana suka ce an batar da N20tr a bankuna.

Gaba daya dukiyar da take yawo a bankuna ba ta kai rabin N89tr ba, Leadership ta rahoto Shehu ya ce da za a samu wadannan kudi, Najeriya za ta biya bashinta.

Martanin Gudaji Kazaure

A baya an ji labari Hon. Gudaji Kazaure ya maidawa Fadar Shugaban kasa da Garba Shehu martani a kan binciko zargin satar Naira Tiriliyan 80 da aka yi.

Kara karanta wannan

Dala 500k/N220m: Tulin miliyoyin da dan Najeriya ya kai banki zai ajiye ya girgiza jama'a

A jawabinsa, ‘Dan majalisar yace irinsu CP Muhammad Wakili (rtd) suna cikin ‘yan kwamitin da suka yi aikin bankado satar da aka tafka a bankunan kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel