Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Kano, Ta Lashe Shaguna 150

Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Kano, Ta Lashe Shaguna 150

  • Gobara mai firgitarwa ta tashi a cikin babbar kasuwar Kachako dake karamar hukumar Takai ta jihar Kano
  • Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa shaguna 150 ne suka kurmushe sakamakon gobarar
  • Ana alakanta tashin gobarar da masu shaye-shaye da suka yadda wuta har ya tashi, an tseratar da shaguna 800

Takai, Kano - Gagarumar gobara ta lashe shaguna dari da hamsin (150) a babbar kasuwar Kachako dake karamar hukumar Takai ta jihar Kano.

Gobara a Kachako
Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Kano, Ta Lashe Shaguna 150. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wannan na kunshe ne a takardar da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya fitar.

Yace lamarin ya auku da tsakar ranar Litinin, jaridar Premium Times ta rahoto hakan.

Takardar da hukumar kashe gobara ta fitar

“Mun samu kiran gaggawa daga hukumar kashe gobara ta yankin wurin karfe 1:13 na rana kuma a take muka tura jami’an ceto wadanda suka isa wurin karfe 1:21 na rana don kashe gobarar dake zagayawa sauran shaguna.

Kara karanta wannan

Kaduna: An Tsinta Gawar ‘Yar Magajiya a Wani Otal dake Zaria, An Fara Bincike

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Girman farfajiyar kasuwar ya kai kafa 2,000 a fadi da tsayin kafa 1,500 a fadi.
“Cike da nasara muka tseratar da shaguna 800 daga wutar.”

- Takardar tace.

Abinda ya janyo gobarar

Yace ana zargin wutar ta fara ne sakamakon wutar da masu shaye-shaye suka saka wa kasuwar.

’Dan kasuwa ya zanta da Legit.ng Hausa

A zantawar Legit.ng Hausa da wani ‘dan kasuwa mai suna Malam Habu, mazaunin Fanisau amma yana zuwa cin kasuwar Kachako, ya sanar da cewa rumfunan da aka kafa ne suka kone.

”Ba a yi wata babbar asara ba gaskiya a gobarar kasuwar Kachako. Rumfunan da aka kafa saboda irinmu masu zuwa cin kasuwa ne suka kurmushe.
”Muna godiya ga Allah da yasa gobarar ba ma’adanar kayayyaki ta taba ba. Allah ya kara kare mu.”

Gobara ta lashe shaguna birjik a Onitsha

Kara karanta wannan

Kamar dai na Buhari: APC ta kirkiri manhajar tattara tallafin kudi daga 'yan Najeriya ga Tinubu

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar Onitsha wacce take a jihar Anambra dake kudancin kasar nan.

An gano cewa kasuwar ta fara ci da wuta ne wurin karfe 2 na dare kuma da gaggawa aka kira jami’an kwan-kwana wadanda tuni suka fara aikinsu.

Wani ‘dan kasuwa ya sanar da cewa ‘Kano Street‘ ce ta kama da wuta wanda kuma Ta Lashe rukunin shaguna har biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da cewa haya jami’an su suna dire a wurin saboda bada tsaro ga kadarori da rayukan jama’a.

Ana ta kokarin kashe wutar wacce tuni ta lashe dukiyoyin miliyoyin Naira amma kuma har zuwa rana wutar bata mutu ba.

Kasuwar Onitsha fitacciyar kasuwa ce da tayi suna kuma take karbar ‘yan kasuwa har daga arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel