Bayan Uwargidar Shugaban Kasa Ta Yafe Masa, Aminu Zai Gana Da Buhari A Villa Yau

Bayan Uwargidar Shugaban Kasa Ta Yafe Masa, Aminu Zai Gana Da Buhari A Villa Yau

  • Aminu wanda yake dalibi a jami'ar tarayya dake Dutse ya fada komar jami'an tsaro ne bayan wata wallafa a shafinsa na Twitter
  • Jama'a da dama dai sunyi kira da uwar gida Aisha Buhari tayiwa Allah ta sa jami'an tsaro da saki yaron
  • Tun makon da ya gabata ne dai jami'an tsaro sukai awon gaba da dalibin bisa zargin cin zarafin matar shugaban kasa

Matashin jihar Jigawan da ya zagi Hajiya Aisha Buhari, uwargidar shugaban kasa, Aminu Mohammed Adamu, ya samu yanci.

Aminu wanda tuni an sakeshi daga kurkukun Suleja zai gana da mijin Aisha, Shugaba buhari kafin ya koma wajen iyayensa, rahoton Leadership.

Wanda ke matsayin Uba ga Aminu, Malam Kabiru Shehu, ya bayyana hakan.

Shehu ya ce Aminu yanzu haka yana Aso Villa kuma yana shirin ganawa da Shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

Yanzu
Bayan Uwargidar Shugaban Kasa Ta Yafe Masa, Aminu Zai Gana Da Buhari A Villa Yau
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran Aminu, dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutsen Jihar Jigawa, zai gana da shugaba Muhammadu Buhari kafin ya a sake shi ga iyalansa.

Mai Aminu Ya Aikata

An kama shi ne da laifin yiwa uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari shagube a sahar Twitter, kuma an gurfanar da shi a asirce a kotu tare da tsare shi a gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja.

Lauyan Aminu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP, ya ce Aminu yana Aso Villa a Abuja yana jiran ganawa da Shugaba Buhari.

A cewar sa

“An saki Aminu. Yanzu haka yana Aso Villa yana jiran ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari".

"Mun yi farin ciki da wannan ci gaban kuma muna farin ciki. Mun matsu da mu sake ganinsa.”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Uwargidan Shugaban Kasa ta Huce, Ta Janye Karar Dalibin da ya ‘Zageta’

Mista Agu ya tabbatarwa da BBC Hausa da yammacin jiya cewa uwargidan shugaban kasar ta janye karar da ta shigar da dalibin

Adamu, wanda dalibi ne a shekarar karshe, ya wallafa wani hoton Aisha Buhari a shafinsa na Twitter da wani rubutu kamar haka “Mama ta ci kudin talakawa ta yi bul bul.”

A farkon makon nan ne mai shari’a Yusuf Halilu na wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Aminu Muhammad.

Muhammad wanda dan asalin garin Azare ne a jihar Bauchi, kuma dalibi ne a shekarar karshe a sashen kula da muhalli.

Da Wanne laifi aka Gurfanar Da Aminu a Kotu

Kamun Aminu ya janyo suka sosai, yayin da kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta nemi afuwar Aisha Buhari a shafinta na Twitter.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Takardar Tuhuma Guda Ɗaya Da Ake Wa Aminu A Kotu Ta Bayyana

Da Wanne Laifi Aka Gabatar Dashi a gaban kotu

Lauyan Aisha Buhari, James Idachaba ya gabatar da daftarin laifin da ake zargin Aminun da aikatawa wanda a ciki yace :

“Kai Aminu Adamu wanda kake namiji kuma kana zaune a unguwar Fulani a Azaren Jihar Bauchi, kayi amfani da @aminullahie aka Catalyst kuma ka rubuta '' Su Mama anchi kudi talakawa ankoshi' wanda hakan in an fassarashi yana nufin "Mama tayi almundahana da kudin talakawa" wanda kuma wannan ya sabawa doka kuma yana da hukunci karkashin sashe na 391 na kundin laifuffuka.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel