Yahaya Bello: Shugaban EFCC Na Ƙasa Ya Sha Alwashin Yin Murabus Daga Muƙaminsa

Yahaya Bello: Shugaban EFCC Na Ƙasa Ya Sha Alwashin Yin Murabus Daga Muƙaminsa

  • Ola Olukoyede ya sha alwashin cewa zai yi murabus daga kujerar shugaban EFCC idan aka gaza gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu
  • Shugaban EFCC ya kuma rantse cewa zai bi diddigin shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi har zuwa lokacin da za a ƙarkare ta
  • Tun farko dai EFCC ta shigar da ƙara gaban kotu tana tuhumar Yahaya Bello da cin amana, zamba da almunhanar N80.2bn

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya rantse da Allah cewa zai bi diddigin kes din tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Mista Olukoyede ya kuma lashi takobin cewa zai yi murabus daga muƙamin shugaban EFCC na kasa idar har ba a gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80

Yahaya Bello da Ola Olukoyede.
Yahaya Bello: Shugaban EFCC ya rantse sai ya gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu Hoto: Alhaji Yahaya Bello, OfficialEFCC
Asali: Twitter

Shugaban na EFCC yi wannan furuci ne yayin hira da ƴan jarida a hedkwatar hukumar EFCC ta ƙasa da ke Jabi a Abuja ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma sha alwashin cewa duk waɗanda suka kawo tangarɗa a ƙoƙarin jami'an EFCC na cafke Yahaya Bello doka za ta yi aiki a kansu.

Yadda EFCC ke kokarin gurfanar da Bello

EFCC na kokarin gurfanar da Bello ne bisa tuhume-tuhume 19 da suka hada da halasta kudaden haram, zamba, cin amana da kuma karkatar da wasu kudade har N80.2m.

Ya ce duk abin da za a yi da adadin sukar da za a yi wa hukumar, shi da mutanensa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa a tsaftace kasar nan.

Olukoyede ya ce hukumar EFCC na bukatar goyon bayan ‘yan Najeriya domin samun nasara, yana mai jaddada cewa idan hukumar ta gaza to Najeriya ta gaza.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya dauki $720,000 ya biya kudin makarantar yaronshi a waje, Shugaban EFCC

A halin da ake ciki, EFCC ta mika kwafin takardar tuhumar da ake yi wa tsohon gwamnan na zambar har N80bn ga lauyansa, Abdulwahab Mohamed, cewar rahoton Vanguard.

Yahaya Bello ya tura saƙo kotu

A wani rahoton kuma Alhaji Yahaya Bello ya shaidawa babbar kotun tarayya mai zama a Abuja cewa a shirye yake ya gurfana gabanta kan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Amma tsohon gwamnan ta hannun ɗaya daga cikin lauyoyinsa ya ce abin da ke hana shi zuwa zaman kotun shi ne tsoron EFCC ta cafke shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel