Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Atiku Ya Nada Ibrahim Zango a Matsayin Babban Sakatare

Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Atiku Ya Nada Ibrahim Zango a Matsayin Babban Sakatare

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nada Ibrahim Zango a matsayin babban sakatare
  • Rahoton da muka samo ya bayyana kadan daga tarihin Zango da kuma irin gudunmawar da ya ba Najeriya
  • 'Yan takara a Najeriya na ci gaba da shirin babban zaben 2023, ba a bar na jam'iyyar adawa ta PDP a baya ba

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nada Ibrahim Zango a matsayin babban sakatarensa.

Nadin Zango na zuwa ne a cikin wata wasika mai dauke sa hannun dan takarar na PDP, kamar yadda Daily Nigerian tace ta samo.

Atiku ya nada wani dan jihar Katsina a matsayin babban sakatarensa
Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Atiku Ya Nada Ibrahim Zango a Matsayin Babban Sakatare | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wanene Ibrahim Zango?

Zango, wanda asalinsa dan jihar Katsina ne ya kasance fitaccen ma'aikacin gwamnati da ya yiwa kasa hidima a ciki da kasashen waje, ciki har a Burtaniya da Saudiyya da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ya kasance babban jami'in kula da harkokin tsaron fadar shugaban kasa tsakanin shekarun 2001 zuwa 2002.

Ya yi digirinsa na farko a fannin tarihi daga jami'ar Sokoto kana ya yi digiri na biyu a fannin huldar kasa da kasa a sashen Anglia Ruskin na jami'ar Cambridge a kasar Burtaniya, jaridar Independent ta ruwaito.

Haka kuma ya samu horo a kwalejin jagoranci na Abshire-Inamori karkashin cibiyar dabaru da nazarin kasashen duniya dake birnin Washington DC a kasar Amurka.

A bangare guda, ya samu horo da dama a fannin gudanarwa, tafiyar da gwamnatin ciki da waje a kasashen waje da ma nan gida Najeriya.

Nadin da Atiku ya yi masa an ce zai fara aiki ne nan take bayan cire wasikar.

Gwamna Obaseki Ya Kori Kwamishinansa Bisa Zargin Ba Ya Tabuka Komai

Kara karanta wannan

Dalilai 5 Dake nuna Peter Obi Ba zai Samu Nasara A Zaben 2023, Fitch Solutions

A wani labarin, gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya sanar da korar kwamishinansa na hanyoyi da gadoji, Engr Newton Okojie bisa zargin baya tabuka komai a aikinsa, Daily Trust ta ruwaito.

Obaseki ya sanar da korar kwamishinan ne a cikin wata sanarwa da kwamishinansa na sadarwa da wayar da kan jama'a, Mr Chris Osa Nehikhare ya fitar a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba a Benin.

Sanarwar ta ce:

“Abin takaici ne yadda ba mu iya samun daman ci gaban da ayyukan hanyoyinmu ba musamman a cikin watanni 12 da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel