Jiragen NAF Sun Yi Lugude Kan ‘Yan Boko Haram, Sun Aike Wasu Lahira

Jiragen NAF Sun Yi Lugude Kan ‘Yan Boko Haram, Sun Aike Wasu Lahira

  • Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai farmakin ba-zata kan ‘yan ta’addan Boko Haram a Banki dake jihar Borno inda suka ragargaza mayakan
  • Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, wannan lamarin ya biyo bayan bayanan sirri da sojojin suka hada tare da yin aiki da shi
  • Wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun yi yunkurin tserewa amma dakarun sun bi su ta jiragen yaki inda suka halaka su tare da wasu kayan aikinsu

Borno - Dakarun sojin saman Najeriya sun yi lugude kan mayakan ta’addancin Boko Haram inda suka halaka da yawa daga cikinsu a Banki dake jihar Borno.

Ruwan wutan da aka yi wa ‘yan ta’addan ta jiragen yaki tare da kular sojin kasa sun kaddamar da aikin da suka yi nufin ragargaza mayakan ta’addancin Boko Haram kuma an yi nasarar halaka wasu a karamar hukumae Bama ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 21 da ‘Yan Bindiga Suka Sace

An tattaro cewa, kungiyar Boko Haram ta fuskanci matsanancin rashin manyan sojojinta a farmakin ranar Juma’a 27 ga watan Oktoba a yankunan Darajamal da Mayenti.

Wata majiyar sirri ta sanar da Zagazola Makama cewa an kaddamar da luguden wutan a ranar Juma’a bayan bayanai gamsassu da aka samu wadanda suka bayyana cewa akwai ‘yan ta’addan masu yawa a yankin.

‘Yan ta’addan kamar yadda binciken Zagazola Makama ya nuna suna boyewa ne a yankunan Bula Ngudoye, Ngori, Kote da Tangalanga, Kulo Gomna, Bulamarwaye, Garje, Wuta, da kauyukan Mordo duk a garuruwa masu iyaka da kamaru.

“Bama-baman da jiragen yakin Super Tukano suka saki sun daki manyan wurare uku da aka yi niyya cike da nasara wanda hakan ya kawo ajalin wasu ‘yan ta’addan da kayayyakinsa da suka hada da motoci kirar Hilux.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace ’yan ta’addan da suka yi yunkurin tserewa an halaka su bayan jiragen yakin sun bi sahun su.

Kara karanta wannan

‘Dan Sanda Ya Sokawa Abokin Aikinsa Almakashi Yayin da Suke Baiwa Hammata Iska

An yi aikin ne bayan amfani da rahotanni daga bayanan sirri dake nuna cewa yankin yana daya daga cikin wuraren da mayakan ke amfani da su wurin kai hari ga sojoji da sauran yankunan Banki.

Ana Tsaka da Fargaba Kan Tsaro, Sojojin Kasa Sun Bayar da Lambobin Kiran Gaggawa

A wani labari na daban, rundunar sojin kasan Najeriya, ta bada lambobi na musamman ga ‘yan kasa domin rahoto tare da kai bayanai kan duk wata barazanar tsaro.

Rundunar sojin kasan ta Najeriya ta wallafa lambobin ne a shafinta na soshiyal midiya a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel