Ortom Ga Atiku: Fulani Ba Za Su Iya Sa Ka Zama Shugaban Kasa Ba

Ortom Ga Atiku: Fulani Ba Za Su Iya Sa Ka Zama Shugaban Kasa Ba

  • Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya gargadi Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP cewa fulani ba za su saka shi ya zama shugaban kasa ba
  • Gwamnan na Benue ya furta hakan ne a matsayin martani ga jawabin da Atiku ya yi a Kaduna inda ya ce shi (Ortom) yana tsangwamar fulani a jiharsa
  • Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin jawabin da ya yi wa wasu matasan jiharsa yana mai cewa Atikun bai yi wa mutanen Benue adalci ba

Benue - Gwamnan Benue, Samuel Ortom, a ranar Laraba, ya yi kira ga dan takarar shugaban kasa na PDP, ya nemi afuwarsa da mutanen jiharsa kan maganganun da ya kansa da mutanen jihar.

Gwamnan ya kuma fada wa Atiku cewa ya dena tunanin fulani kadai za su iya saka shi ya zama shugaban kasa, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Ortom ya Gindayawa Atiku Abubakar Sharadi 1 na Samun Kuri’un Benuwai

Ortom da Atiku
Ortom Ga Atiku: Fulani Ba Za Su Iya Sa Ka Zama Shugaban Kasa Ba. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Ortom ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa matasa jawabi a yankin Jemgbagh da suka hada da kananan hukumomin Gboko, Buruku da Taraka da suka nuna goyon bayansu gare shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bata wa gwamnan rai ne yayin wani taro da kungiyar tuntuba ta arewa ta shirya a Kaduna inda shi (Atiku) ya zargi Ortom da tsangwamar fulani.

Martanin Ortom

Amma, Ortom a ranar Laraba ya musanta cewa yana tsangwamar makiyaya Fulani kuma ya yi ikirarin cewa mutanensa sun sace shanu daga gonarsa.

Ortom ya ce ya tuntubi Atiku ta manhajar WhatsApp kan batun kuma ya bashi hakuri amma ya ki fitowa fili ya bada hakurin, ya kara da cewa ba zai yarda da hakan ba.

Wani sashi na kalamansa:

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ta karewa Atiku, gwamnan Arewa na PDP da dattawan jiharsa sun ce ba sa yinsa

"Ban taba cewa dukkan fulani mutanen banza bane. Abokai na ne, har daki na suna iya shiga. Ban taba korar fulani ba.
"Amma ban yarda da yan ta'addan fulani da ke zuwa daga Chadi, Senegal da Mali ba. Dole ya janye maganar, idan bai yi hakan ba, ranar zabe za mu jefa kuri'ar mu yadda zaben ta zo.
"Ba za mu iya zaben shugaban kasa da zai cigaba da kashe mutanen mu ba. Yana son ya yi amfani da don misali. Atiku bai yi wa mutane adalci ba. Kana tunanin fulani za su sa ka zama shugaban kasa, ka yi karya. Ka yi sabo ga mutanen Benue."

Asali: Legit.ng

Online view pixel