Maganin a gonar yaro: Maganin ciwon koda da hawan jini a saukake

Maganin a gonar yaro: Maganin ciwon koda da hawan jini a saukake

Wani mai bincike a harkar lafiya Alkasim Muhammad Baban Manar ya zakulo wasu fa'idoji na amfani da Kankana wajen maganin wasu cututtuka da suke addabar mutane a matakin riga kafi

Maganin a gonar yaro: Maganin ciwon koda da hawan jini a saukake
Maganin a gonar yaro: Maganin ciwon koda da hawan jini a saukake

Kankana daya ce daga cikin 'ya'yayen bishiyoyi masu zaki da suke yi a lokacin bazara, sai dai yanzu kusan ana samunta a kowani yanayi ma, tana cikin 'ya'yayen bishiya da ba sa yankewa, irin su lemo, an fara sanin Kankana ne a kasashe masu zafi irin su Afrika da India, kafin ma su tsallaka zuwa qashen dake zagaye da tekun tsakiya wato Mediterranean, daga nan sai ta karsa Europe da kudancin Amurka.

Wani abin da zai ba ka mamaki shi ne ba duk masana ne suka amince da cewa kankana dan bishiya ce ba, wasu daga cikin manya-manyan masu bincike suna ganin cewa ana sakata a cikin ganyayyaki ne kamar su Cucumber sai dai tana da zaki, ana samunta a ko'ina cikin nau'uka da launuka mabambanta, wanda har jami'ar Washington da ke Amurka ta fitar da wasu alkaluma inda take cewa akwai nau'o'in kankana a duniya har 126 dukkansu suna dauke ne da nau'o'i kala daban-daban.

Kankana kusan dukkanta ruwa ne don gwargwadon ruwan dake cikinta an qiyasta ya kai 90%-99%, sukarin da ke cikinta kuwa zai kai 8%, sannan ana samun vitamin C da vitamin B a cikinta, kamar yadda ta tattara sinadarin Sulphur, Calories, Phosphor da kuma Potassium, wani kuskure da wasu suke yi shi ne suna cire 'ya'yan kankanan a lokacin da suke sha, ba su san cewa kamata ya yi su tauna ba, 'ya'yan ba su da daci sai dandanon mai dadi ga Fat 43%, Sugar 16%, sai Protein 27.

Duk da cewa akwai kankana kala daban-daban a duniya amma ku san dukkansu suna da sinadaran kara kuzari (wato Vitamins) da sauran ababan gina jiki kamar Protein, Calcium, Iron, Sodium, Magnesium, Phosphor, Potassium, da kuma sauran Vitamins A, da C, zai yi kyau mu waiwayi wasu fa'idojin da kankanar ke yi ga lafiyar dan adam.

1. KODA:

Kankana ta kan taimaka wa koda matuka, domin ruwan da ke cikinta, kamar dai yadda aka sani takan saukake wa taruwar fitsari da fitarsa, wannan sabo da tana da sinadarin Potassium wanda ya ke taimakawa wajen korar gurbataccen sinadari daga jukkunammu, sannan sinadarin yana rage yawan sinadarin Hyperuricemia a cikin jini.

2. FATAR DAN ADAM

Dangane da fatar da adam, sananne ne cewa kankana tana da sinadarin da ya ke kare jikin dan adam daga Oxidation, don haka ne ma take iya fatattakar tsattsakar fata, da lalacewarta, takan ba wa fata kariya daga hasken rana mai cutarwa, masamman yadda take dauke da sinadarin Lycopene da Crotin wadan da suke taimakawa wajen kare jikin dan adam daga kunar ranar da take sanya cutar fata ko koma cancer wace take samun fatar.

3. HAWAN JINI

Sai kuma mutane masu fama da mummunar bugawar jini, kankana takan taimaka musu sabo da tana kunshe da sinadarai kamar su Manganese da Potassium masu aiki wajen tsara bugawar jinin, matuqar kankana ta qumshi wadannan sinadaran kenan ta dace da mutum mai fama da hawan jini ya riqe ta a matsayin qari cikin abincin da yake iya ci a kullum.

4. CIWON SUGAR

Kamar dai yadda muka fadi ne a baya cewa kankana ta qumshi sinadarin Potassium da Magnesium wadan da aikinsu shi ne taimaka wa jiki wajen tato sinadarin Insulin wanda yake tsara wa sukari yadda zai yi aiki a cikin jini, qarancin wannan sinadari shi yake hana iya sarrafa sinadarin Glucose da mutum ya samu a jikinsa ta hanyar wasu abinci masu masifar zaqi, ko wurin wasu 'ya'yayen bishiyar, a nan cin kankanan zai taimaka wa mai cutar ko ta ba wa wanda bai da ita wata kariya.

6. KUZARIN JIKI

Ana aiki da kankana a matsayin wata madogara ta dabi'a wace take maye makwafin wasu magunguna masu kara wa mutum kuzari a jiki da qarfi da lafiya, wadan da galibin 'yan wasan motsa jiki su suke amfani da su, domin kankana tana da dauke da Potassium da Magnesium da kuma Vitamin B da nau'o'insa wanda shi kuma yake qara kuzarin jiki.

7. MATSALOLIN IDO

Kankana takan taimaka wa ido wajen kare ganin mutum, don tana dauke da Vitamin A wanda yake da mahimci ga idon mutum, wani bincike ya gano cewa in dai mutum zai sanya kankana a gaba kullum zai ci na kimanin yankar N100 a yau, to ba ko shakka kankana za ta taimaka masa wajen kyautata ganinsa masamman domin wadan da ganinsu yake raguwa a dalilin aiki da na'urorin zamani kamar su talabijin, wayoyi da kwafyuta, ko kuma don tsufa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng