Zan Kawo Karshen Ta'addancin Yan Bindiga a Kaduna Idan Na Ci Zaben 2023, Atiku

Zan Kawo Karshen Ta'addancin Yan Bindiga a Kaduna Idan Na Ci Zaben 2023, Atiku

  • Atiku Abubakar ya kara ɗaukar muhimman alƙawurra a wurin gangamin kamfen PDP da ya gudana a Kaduna
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi alƙawarin kawo karshen yan bindiga da farfaɗo da harkar Masana'antu a Kaduna
  • A dazu ne wasu yan daba suka kai wa magoya bayan PDP a wurin kamfen Kaduna amma jami'an tsaro suka shiga tsakani

Kaduna - Atiku Abubakar, mai fafutukar zama shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, ya sha alwashin farfaɗo da masana'antu a jihar Kaduna idan har ya lashe zaɓen 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya yi alƙawarin kawo karshen ayyukan yan bindigan daji da suka hana jihar zaman lafiya tsawon shekaru.

Atiku Abubakar a Kaduna.
Zan Kawo Karshen Ta'addancin Yan Bindiga a Kaduna Idan Na Ci Zaben 2023, Atiku Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Da yake jawabi a wurin gangamin taron yakin neman zaɓensa wanda ga gudana a filin Ranches Bees stadium, Kaduna, Wazirin Adamawa ya gode wa mazauna jihar bisa ba shi adadi mai yawa na kuri'u a zaɓen 2019.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Yi Martani Kan Harin Wasu 'Yan Daba a Wurin Kamfe Ɗinsa a Kaduna, Ya Tura Sako Ga Buhari

Ya kuma yi alƙawarin ɗaukar matsalolin Kaduna dagaske idan har mazauna suka fito kwansu da kwarkwata suka kaɗa masa kuri'unsu kuma suka tabbatar ya samu nasara a zaɓen 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabinsa yace:

"Bari na fara da gode muku bisa goyon bayan da kuka bani a 2019, ku ne kuka bani kuri'u mafi yawa a zaɓen 2019 kuma ina da yakinin zaku sake amince mun a wannan karon."
"Na zo nan a madadin jam'iyyar PDP domin na muku albishir da cewa idan kuka zaɓe mu, zamu kawo karshen matsalar tsaro a Kaduna. Zamu farfaɗo da masana'antu tare da taimakon bangaren masu zaman kansu a Kaduna."

Mu gode Allah da ya bamu Atiku - Gwamna Okowa

A nasa ɓangaren, abokin takarar Atiku, Gwamna Okowa na jihar Delta yace mutanen kudancin Najeriya sun shirya dangwalawa Atiku bayan nasarar PDP a zaɓen gwamnan jihar Osun.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Ba Da Mamaki, Ta Lashe Zaben Ciyamomi 30 da Kansiloli a Wata Jiha

"Ina gode wa Allah da ya bamu Atiku wanda ke da hanyar warware matsalolin Najeriya. Idan muka samu Atiku a matsayin shugaban ƙasa ba zamu sake kwana da yunwa ba kuma ya shirya kawo karshen yan bindiga a arewa."

A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya Nemi Atiku Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa a 2023

Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya nemi Atiku Abubakar ya janye daga takara a 2023.

Tsohon gwamnan Legas ɗin ya bukaci Atiku ya saka masa da karamci ta hanyar aje tikitin PDP, ya mara masa baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel