Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

  • Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi ya angwance da kyakkayawar mata ta uku makonni kadan bayan aurensa da attajira Mariam Ajibola Anako
  • Bidiyon bikin basaraken da tsohuwar sarauniyar kyau, Tobi Phillips, ya karade shafukan soshiyal midiya
  • Yan Najeriya a yanar gizo sun tofa albarkacin bakunansu kan sake auren da basaraken kasar Yarbawan yayi

Jama’a na ta cece-kuce a shafukan soshiyal midiya kan aure-auren da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ke yi a baya-bayan nan.

Yan makonni bayan ya auri matarsa ta biyu, attajira Mariam Ajibola Anako, babban basaraken kasar yarbawan ya sake auren mata ta uku mai suna, Tobi Phillips.

Ooni na Ife
Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni Kadan Hoto: @thetattleroomng/@ooniadimulaife
Asali: Instagram

An gudanar da bikin auren wanda ya samu halartan makusanta a ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba.

Wani bidiyo daga shagalin bikin ya bayyana a soshiyal midiya kuma ya haifar da martani daban-daban daga jama’a.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amaryar Ooni ta uku ta kammala karatunta a bangaren kimiyyar ruwa daga jami’ar Lagas.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

thaworldbanana tace:

“Kuma matan suna ta yarda da auren? Saboda yin suna na wucin gadi ko me?”

abasidocapon yace:

“Wasu mutane na manta cewa wannan sarki ne na Afrika…ku daina furta shirme yana da yancin auren mata da yawa idan har zai iya daukar dawainiyarsu.”

nenejones_esq tace:

“Shin wani zai iya yi mun bayanin dalilin da ke tattare da wannan aure na mata da yawa?”

myguy757 tace:

‘”Wani abu na damun sarkin nan. Kuma wani abun na damun suma matan da ke aurensa.”

Awanni 24 Bayan Ya Yi Sabuwar Amarya, Ooni Na Ife Zai Sake Yin Wuff Da Wata Kyakkyawar Budurwa

A baya mun ji cewa kimanin sa’o’i 24 da yin sabuwar amarya a fadarsa, mai martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, ya kammala shiri tsaf domin sake angwancewa da wata budurwa.

Kara karanta wannan

Cikakken Jawabin da 'Dan takaran APC, Bola Tinubu ya yi Daga Shigowa Najeriya

A yammacin ranar Talata ne aka shigar da amarya Olori Mariam Anako, fadar Ile-Ife bayan an kammala duk wasu bukukuwan al'ada.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wata tawaga ta musamman daga fadar Ile-Ife da ke jihar Osun sun ziyarci dangin mai shirin zama amaryar, Dr. Elizabeth Opeoluwa Akinmuda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel