Auren Cin Amana Tsohuwar Matar Adam Zango Tayi, Jaruma Safna Ta Fasa kwai

Auren Cin Amana Tsohuwar Matar Adam Zango Tayi, Jaruma Safna Ta Fasa kwai

  • Jarumar Kannywood, Sapna Aliyu Maru, ta yi bayani dalla-dalla akan auren cin amanar da kawarta, Maryam AB Yola tayi a makon da ya gabata
  • Yayin zantawa da Mujallar Fim, ta bayyana cewa wanda aka ga Maryam ta aura a wasu bidiyo da ta bayyana, asali saurayinta ne
  • A cewarta, auren ya yi matukar bata mamaki kasancewar kawarta ce wacce su ke da matukar kusanci amma bata kalli hakan ta daga mata kafa ba

Sapna Aliyu Maru, jaruma a masana’antar Kannywood, ta bayyana yadda kawarta, Maryam AB Yola ta aure mata saurayinta duk da su na da kusanci.

A wata tattaunawa da tayi da Mujallar Fim, bayan daurin auren Maryam da kuma matashin mai suna Muhammad Murtala, ta ce an ci amarta ne.

Marya AB Yola
Auren Cin Amana Tsohuwar Matar Adam Zango Tayi, Jaruma Safna Ta Fasa kwai. Hoto daga @ab_yola_beauty_skin_care
Asali: Twitter

Ranar Juma’a, 30 ga watan Satumban 2022, ne aka ga Maryam din ta wallafa wani bidiyo tare da wani dan kasuwa kuma dan jarida da ke kasuwanci a tsakanin Legas da Fatakwal.

Kara karanta wannan

Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola

Dama Maryam fitacciyar jaruma ce a Kannywood, kuma bidiyon auren nata ya yadu ne bayan ta wallafa bidiyoyi biyu na bikin, daya ita kadai, dayan kuma da angonta cike da farinciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nan da nan mutane su ka hau taya ta murna akan wannan babban al’amari da ci gaban da ya same ta.

Sai dai Sapna ta ce tabbas Maryam ta ci amanarta saboda sun dade da shiryawa da Muhammad akan yadda za su gudanar da aurensu.

A cewarta, ta yi mamakin yadda Maryam din taci amanarta kasancewar su na da kusanci mai yawa da ita. Ba ta kara wani bayani ba bayan wannan ikirarin da tayi.

Maryam tsohuwar matar Adam A. Zango ce. Akwai wata majiya da ta shaida wa Mujallar Fim cewa Maryam din ta taba aure bayan rabuwarta da Adam Zango, amma auren bai dade ba su ka rabu.

Kara karanta wannan

Kana Da Kyau: Budurwa ‘Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Saurayi A Cikin Banki, Ta Karbi Lambar Wayarsa

Tsohuwar Matar Adam Zango, Maryam AB Yola Tayi Aure, Kyawawan Bidiyoyinta da Ango Sun Dauka Hankali

A wani labari na daban, tsohuwar matar fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, Maryam AB Yola ta yi auren ba-zata a ranar Juma'a da ta gabata.

Kamar yadda jarumar da kanta ta wallafa bidiyoyinta tare da kyakyawan angonta a shafinta na Instagram mai suna @ab_yola_beauty_skin_care, ta sanar da masoyanta cewa a yanzu fa ta zama matar Muhammad.

A ranar Juma'a da yammaci ta daura wani bidiyonta ta sha lalle sanye da kayan amare. Kallon bidiyon ga duk wanda ya saba bibiyarta a shafinta na Instagram, za a iya cewa iya adonta ne da ta saba don dama can 'yar kwalisa ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel