Wanka Kullum Asarar Ruwa Ne: Bidiyon Kyakyawar Budurwar da Tayi wata 1 Babu Wanka

Wanka Kullum Asarar Ruwa Ne: Bidiyon Kyakyawar Budurwar da Tayi wata 1 Babu Wanka

  • Wata matashiyar budurwa ta haddasa cece-kuce bayan bayyana cewa ta shafe tsawon makonni hudu bata yi wanka ba
  • Yayin da take nanata cewa ba dole sai mutum yayi wanka kullun ba kafin yaji daidai a jikinsa, budurwar ta bayyana dalilin da yasa ya zama haka a gareta
  • Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun ki yarda da ikirarin nata, yayin da wasu ke ganin haka a matsayin kazanta

Wata budurwa da tayi ikirarin cewa ta shafe tsawon wata guda babu wanka ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya.

A wani bidiyo wanda ya yadu a TikTok wanda a ciki ne ta bayyana hakan, budurwar ta ce ita ta tabbatar cewa ba sai mutum yayi wanka kullun bane zai ji dadi.

Budurwa
Wanka Kullum Asarar Ruwa Ne: Bidiyon Kyakyawar Budurwar da Tayi wata 1 Babu Wanka Hoto: TikTok/@slickvicwilliams
Asali: UGC

Jama’a sun soki furucin nata, inda wasu da dama suka nuna shakku kan ikirarin nata kuma hakan yasa ta yin martani a sashin sharhi.

Kara karanta wannan

Mai kamar maza: Bidiyon budurwa mai tuka tirela ya girgiza intanet, jama'a sun shiga mamaki

Da take kare bidiyonta, matashiryar ta ce rashin yin wanka kullun na taimakawa wajen rage barnar ruwa a yankinta wanda ke fama da fari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Domin biyan bashin wankan da bata yi ba, budurwar kan je rafi wanka.

“Duk ina zuwa yin iyo a ruwa sosai don haka ina ganin hakan ma wanka ne a kimiyance.
“Kuma hakan na rage barnar ruwa a lokacin fari.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Kieron Stewart ta ce:

"A'a Iyo a ruwa baya nunawa saboda ta yaya kike kashe datti da maiko? da sabulu."

user5108503656720 ya ce:

"Kamar kin je daga hannayenki sama sai wayarki ta mutu..."

Misszazax__ ta ce:

"Ita kanta wayar taba yarda ba sannan ta mutu, bata son kasancewa cikin wannan tatsuniyar."

Cacherel ya ce:

"Kalli wayarki na gudu."

Kara karanta wannan

'Yar kirki: Bidiyon tsaleliyar budurwar da ke taya mahaifiyarta soya garin rogo ya jawo cece-kuce

Amarya Ta Sharbi Kuka A Wajen Baikonta Yayin da Mahaifiyarta Ta Kawo Mai Daukar Hoton Kauye, N10,000 Ya Karba

A wani labarin, wata kyayyawar amarya yar Najeriya ta fusata sosai a yayin baikon aurenta a yankin Offa da ke jihar Kwara.

Budurwar mai suna Aisha Odunola a Twitter, ta ce mahaifiyarta ta dauka mai hoto wanda sam bai kware ba don yin aiki a wajen taron.

Kyakkyawar amaryar ta yo hayar wani kwararren mai daukar hoto sannan ta bukaci mahaifiyar tata ta tawo dashi idan za ta zo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel