Bauchi: Raba Mata Da Maza A Makarantun Sakandare Ya Harzuka Dalibai, Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zanga

Bauchi: Raba Mata Da Maza A Makarantun Sakandare Ya Harzuka Dalibai, Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zanga

  • Dalibai sun fita titunan jihar Bauchi suna zanga-zangan zumana kan sabuwar tsarin raba mata da maza a makarantun sakandare
  • Mr Aliyu Tilde, kwamishinan ilimi na Jihar Bauchi ya ce an bullo da dokar ne domin magance tabarbarewar tarbiyya a makarantun sakandare na jihar
  • Tilde, wanda ya ce za a aiwatar da sabon tsarin a duk inda zai yi wu ya kuma yi kira ga makarantu masu zaman kansu su raba mata da maza

Jhar Bauchi - Daliban makarantun sakandare a halin yanzu suna zanga-zanga a titunan Bauchi kan wata sabuwar doka da gwamnati ta kawo na raba mata da maza a makarantu.

Dalibai sun koma makaranta ne a hukumance yau (Litinin) a sassan jihar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Akeredolu: Babu Gudu Babu ja da Baya kan Shirin Ba Sojojin Amotekun Makamai

Dalibai na tattaki
Ana Zanga-Zanga Saboda Raba Dalibai Mata Da Maza A Bauchi. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Mr Aliyu Tilde, ya ce gwamnatin jihar ta kammala shiri don raba dalibai mata da maza a makarantun jihar.

Za a kaddamar da dokar ne wurin da zai yi wu - Tilde

Tilde, yayin jawabin da ya yi wa manema labarai bayan taron majalisar zartarwa na jihar, SEC, a Bauchi, ya ce za a aiwatar da dokar ne a inda aka ga zai yi wu.

An bullo da tsarin ne don inganta tarbiyya

Kwamishinan ilimin ya yi bayani cewa an bullo da tsarin ne domin magance tabarbarewar tarbiyya da ya zama ruwan dare tsakanin daliban makarantun sakandare.

A cewarsa, ana fatan makarantu masu zaman kansu da ke jihar za su yi koyi da tsarin su raba maza da mata a makarantunsu, maza su rika zuwa makaranta daya, mata su rika zuwa wata daban.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

Muna goyon bayan tsarin dari bisa dari, In Ji Maikano

Wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi wani malamin makarantar sakandare a Bauchi don jin ra'ayinsa kan sabuwar tsarin.

Abdullahi Maikano, malami a makarantar sakandare ta GGSS Nasarawa, Azare a Bauchi ya ce yana goyon bayan tsarin saboda munanan halaye da ke faruwa a makarantun da ake gwamutsa mata da maza.

Ya ce:

"Ana samun karuwar abubuwa marasa kyau tsakanin mata da maza, har rubutu a jikin hijabin mata maza ke yi a lokacin kammala karatu.
"Ga shi suna bude dandalin hira a soshiyal midiya inda babu wanda ya san irin harkar da ake yi a irin wannan wuraren.
"Duba da cewa yara ne, yana da kyau a dauki matakan da za su daidaita musu tarbiyya don haka ina goyon baya."

Maikano ya kara da cewa makarantar da ya ke koyarwa maza da mata ne ke gwamutse amma a yanzu an raba ta zama mata zalla kuma ya ji dadin hakan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da bam ya tashi bayan sallar Juma'a, mutane da dama sun mutu

Hakazalika, Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu daga cikin daliban da suka yi wannan zanga-zangar amma kawo yanzu ba su amsa sakon kar ta kwana da aka aika musu ba kuma ba su daga waya ba.

Korar Malaman Makaranta da El-Rufa'i ya yi a Kaduna ya saɓa wa doka, NUT

A wani labarin, Shugaban ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) reshen jihar Kaduna, Ibrahim Ɗalhatu, ya yi Allah waɗai da matakin korar malamai 2,357 a Kaduna bayan faɗuwa jarabawar cancanta.

Jaridar Vanguard ruwaito cewa Ɗalhatu ya ayyana matakin da gwamnatin Kaduna ta ɗauka da ya saɓa wa doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel