Mahaifiyar Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, Ya rasa Mahaifiyarsa

Mahaifiyar Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, Ya rasa Mahaifiyarsa

  • Allah yayi wa mahaifiyar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, rasuwa a yau Lahadi, 18 ga watan Satumba
  • Kamar yadda ya sanar a Abuja, Hajiya Bintu Jamarema ta rasu tana da shekaru 92 bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Za a yi jana'izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar da karfe 5 na ranar Lahadi a Maiduguri

FCT, Abuja - Mahaifiyar tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, Ibrahim Magu, ta kwanta dama.

Hajiya Bintu Jamarema ta rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya da tayi yayin da take shekaru 92 a duniya, jaridar The Nation ta rahoto hakan.

Magun EFCC
Mahaifiyar Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, Ya rasa Mahaifiyarsa. Hoto daga thenationonline.net
Asali: UGC

A wata takarda da Magu ya fitar a Abuja, tace:

"Daga Allah muke, kuma gare shi za mu koma. Ina sanar da mutuwar mahaifiyata, Hajja Bintu Jamarema mai shekaru 92.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Hadimin Gwamnan Kaduna da Mambobin APC Sama da 13,000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ta rasu a yau Lahadi, 18 ga watan Satumban 2022 a garin Maiduguri bayan gajeriyar rashin lafiya.
"Za a yi jana'izarta da karfe 5 na yamma da izinin Allah. Allah ya yafe mata kura-kuranta kuma ya sanya ta a Aljannah Firdausi. Ameen Thumma Ameen."

'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

A wani labari na daban, wani mutun 'dan kasar China ya sokawa budurwarsa mai shekaru 23 wuka inda ta mutu a take a kwatas din Janbulo dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Lamarin ya faru ne wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan wanda ake zargin ya kai wa budurwa mai suna UmmaKulsum Sani Buhari ziyara a gidan iyayenta dake kusa da ofishin National Environmental Standards and Regulations Enforcement Agency (NESREA).

Kara karanta wannan

Yadda saurayin diyata dan China ya shiga har gida ya caccaka mata wuka, inji mahaifiyar Ummita

Yayin da abinda ya hada masoyan biyu har yanzu ba a gano shi ba, Daily Trust ta tattaro cewa likitoci sun tabbatar da mutuwar budurwar.

Abubakar Mustapha, wanda makwabci ne ga mamaciyar, ya sanar da Daily Trust cewa bazawara ce kuma wanda ake zargin saurayinta ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel