Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Hadimin Gwamna Bauchi, Sun Jikkata Wani

Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Hadimin Gwamna Bauchi, Sun Jikkata Wani

  • Waau miyagun yan bindiga sun kai farmaki gidan mai taimaka wa gwamnan Bauchi kan harkokin addinin Kirista, Fasto Magaji
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun je da nufin kisa amma Allah ya tseratar da shi, sun jikkata wani matashi
  • Tuni dai tawagar ma'aikatar harkokin Addinai ta jihar Bauchi ta je har gida domin jajanta masa

Bauchi - Hukumar yan sanda reshen jihar Bauchi ta tabbatar da cewa wasu miyagu sun yi yunkurin halaka babban mai taimaka wa gwamna kan harkokin Addinin Kirista, Fasto Zakka Luka Magaji.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun kai farmaki gidan Fasto Magaji dake ƙauyen Birshi, birnin Bauchi da wata mummunar manufa.

Harin yan bindiga a Bauchi.
Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Hadimin Gwamna Bauchi, Sun Jikkata Wani Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa yayin harin, yan bindigan sun jikkata wani mutumi ɗan kimanin shekara 32 a duniya wanda ke zama tare da Fastor Magaji a gidan.

Da yake jawabi yayin da ya karɓi baƙuncin kwamishinan harkokin Addinai, Hon. Umar Babayo Kesa, wanda ya jagoranci zuwa jaje, Hadimin gwamna ya labarta yadda harin ya auku da cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ni suka nufa duk da bansan abinda suka kudurta a zuciyoyinsu ba amma Allah ya nuna ikonsa, mutumin da ya samu rauni yana samun sauki a yanzu."

Kwamishinan yace sun ziyarci Fasto Magaji ne domin jajanta masa kan abinda ya faru, inda ya yi Addu'a Allah ya cigaba da kare shi da sauran 'yan gidansu daga sheɗanun mutane.

Magaji ya gode wa kwamishina da baki ɗaya jagorancin ma'aikatar harkokin Addinai, yace, "Wannan alama ce dake nuna zaman lafiya ya samu gindin zama tsakanin mutanen jihar nan karkashin jagorancin gwamna Bala Muhammed."

Yadda Lamarin ya faru

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakili, yace hukumar ta samu kiran gaggawa da ƙarfe 1:00 na rana cewa yan bindiga aƙalla 7 sun farmaki gidan Fasto Magaji.

"Nan take bayan samun kiran, kwamishinan yan sanda ya umarci dakaru karkashin jagorancin DPO suka kai ɗauki, inda maharan suka tsere cikin jeji."

SP Wakil ya ƙara da cewa jami'ai sun yi gaggawar ɗaukar wanda ya jikkata zuwa Asibitin koyarwa na jami'ar ATBU domin kulawa da lafiyarsa.

Ya tabbatar da cewa dakaru sun ƙara zafafa sintiri ta ko ina a yankin tare da yi wa dazuka tsinke da nufin cafke waɗanda suka kai harin.

A wani labarin kuma Jirgin Yakin Soji Ya Halaka Bashir Iblis da Wasu Ƙasurguman Yan Ta'adda a Arewa

Jirgin yaƙin rundunar sojin Najeriya ya samu gagarumar nasara a wani samame da aka kai mafakar mayaƙan ISWAP a Borno.

Zakazola Makama, yace luguden wutan jirgin ya yi ajalin ƙusoshin kungiyar guda uku da tarin mayaƙa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel