Matashi Ya Bayyana Wa Yan Sanda Yadda Ya Ke Amfani Da Farin Takarda Wurin Damfara Masu POS

Matashi Ya Bayyana Wa Yan Sanda Yadda Ya Ke Amfani Da Farin Takarda Wurin Damfara Masu POS

  • Yan sanda a jihar Anambra sun yi nasarar cafke wani matashi da ake zargi da damfarar masu sana'ar POS
  • Wanda ake zargin ya amsa cewa yana amfani da farin takarda da ya yanka su kamar girman kudi yana damfarar masu POS din
  • Yan sandan sun ce suna cigaba da bincike kuma za su kamo sauran abokan harkallar wanda ake zargin

Anambra - Rundunar yan sanda ta kama wani matashi dan shekara 26 kan zarginsa da amfani da asiri wurin damfarar masu sana'ar biyan kudi na POS a jihar, rahoton Premium Times.

Kakakin yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Taswirar Jihar Anamba
Matashi Ya Bayyana Wa Yan Sanda Yadda Ya Ke Amfani Da Farin Takarda Wurin Damfara Masu POS. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Karbi N19m, Da Kwale-Kwale A Matsayin 'Harajin Tsaro' Daga Mutanen Wasu Garuruwa A Zamfara

Wanda ake zargin, Chisom Nweke, wanda aka kama a ranar Alhamis, dan asalin garin Umuawulu ne, wani gari da ke karamar hukumar Awka a jihar.

Yan sandan sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana amfamni da asiri wurin damfarar masu POS a Akwa da garuruwan da ke makwabtaka da su.

Wanda ake zargin mamba ne na wata tawagar bata gari da suka kware wurin aikata laifuka, in ji yan sandan.

Mr Ikenga ya ce:

"Binciken farko sun nuna cewa wanda ake zargin yana yanka fararen takarda dai-dai girman kudi sai ya bawa masu POS a matsayin kudi da za su tura masa."

Su kuma masu POS din, saboda asirin da ya musu za su karbi takardun a madadin kudi daga hannun wanda ake zargin.

Kakakin yan sandan ya ce ana bincike don gano sauran mambobin kungiyar bata garin da ke aiki tare da shi.

Damfara Ta N26.7m: Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Maka Mataimakin Kwamandan NSCDC a Kotu

Kara karanta wannan

An Kama Mutune 5 Kan Kisar Dan Sanata Kabiru Gaya Mai Wakiltar Kano, An Samu Karin Haske Kan Dalilin Kisarsa

A wani rahoton, ICPC ta yi karar wani mataimakin kwamanda na hukumar tsaro ta NSCDC, Edike Mboutidem Akpan a wata babban kotun tarayya a Abuja kan zarginsa da amfani da kamfanin dillancin gidaje, Danemy Najeriya Ltd, don damfarar kwastomomi zunzurtun kudi har N26,655,000.

Mai magana da yawun hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Daily Trust ta rahoto Ogugua ya ce an gurfanar da wanda ake zargin a gaban Mai shari'a V.S. Garba kan tuhuma guda 17.

Asali: Legit.ng

Online view pixel