Ba Makiyaya Fulani Ke Kisa Ba, Baƙi Ne Suka Shigo Nigeria, Gwamna Ikpeazu

Ba Makiyaya Fulani Ke Kisa Ba, Baƙi Ne Suka Shigo Nigeria, Gwamna Ikpeazu

- Gwamna jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya ce ba makiyaya Fulani ke kai hare-hare a Nigeria ba

- Ikpeazu ya ce baki ne daga kasahen ketare kamar su Chadi da Mali ke shigowa suna kisa a Nigeria

- A cewarsa ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali kan tattara bayannan sirri da bincike a maimakon siyan makamai

Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Abia ya ce wasu mutane daga kasashen waje ne ke kashe kashe a Nigeria ba makiyaya Fulani bane, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke magana da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin ziyarar da ya kai gidan talabijin na TOS.

Ba Makiyaya Fulani Ke Kisa Ba, Baƙi Ne Suka Shigo Nigeria, Gwamna Ikpeazu
Ba Makiyaya Fulani Ke Kisa Ba, Baƙi Ne Suka Shigo Nigeria, Gwamna Ikpeazu.
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yi Wa Yayan Sarkin Musulmi Rasuwa

Ikpeazu ya ce a maimakon a rika kashe kudin wurin sayan makamai kawai, ya kamata gwamnatin tarayya ta fi kashe kudade kan tattara bayannan sirri.

Ya ce bayannan sirrin za su saka gwamnati ta gane cewa ba makiyaya fulani bane ke kisar amma wasu daga kasashen waje ne da suka shigo cikin Nigeria.

A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta kashe kashi 65% na kudade wurin tattara bayannan sirri da bincike sai kashi 30% kan sayan makamai domin makiyan ba kayan yaki suke saka wa ba da za a gane su.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

"Me yasa muka kasa ganewa cewa wasu sunyi kutse a kasarmu? Babu wani abu mai suna makiyaya fulani masu kisa, akwai mutane daga kasashen Chadi, Mali da suka shigowa Nigeria. Ba yan Nigeria ke kashe yan Nigeria ba. Wasu daga waje ke shigowa. Ya kamata mu kashe kude kan kula da shige da fice," wani sashi cikin jawabinsa.

Gwamnan ya ce ya kamata a fayyace su wanene makiyan Nigeria domin hakan zai taimaka wurin magance kallubalen rashin tsaro.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel