Iyalan Tukur Mamu Wanke Shi Daga Zargi, Sun Bayyana Wanda Ke Da Kayan Sojojin Da DSS Ta Gano A Gidansa

Iyalan Tukur Mamu Wanke Shi Daga Zargi, Sun Bayyana Wanda Ke Da Kayan Sojojin Da DSS Ta Gano A Gidansa

  • Yan uwan Malam Tukur Mamu mawallafin jaridar Desert Herald a Kaduna sun yi karin haske kan kayan sojoji da DSS ta ce ta gano a gidansa
  • Iyalan mai sasancin da yan bindigan sun ce kayan sojojin na wani dan Mamu ne, mai suna Yahaya Bello wanda ya kammala karatunsa a NDA
  • A yayin da yan sandan farin kayan ke cigaba da tsare Mamu da dansa Faisal, sun kuma kama surukunsin mai suna Abdullahi Mashi

Jihar Kaduna - Iyalan mai tattaunawa da yan ta'adda don ceto mutane, Tukur Mamu sun yi martani kan kayan sojoji da aka gano a gidansa suna mai cewa na dansa ne, jami'in sojan ruwa.

Hakan na cikin wata sanarwa ne da Ibrahim Mada ya fitar kuma ya raba wa manema labarai a Kaduna, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike

Malam Tukur Mamu.
Iyalan Tukur Mamu Sun Fayyace Gaskiya Game Da Kayan Sojoji Da DSS Ta Gano A Gidansa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalan kuma sun yi kira ga DSS su dena yi wa Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna 'shari'ar shafukan watsa labarai.

Kayan sojoji da DSS suka gano na dan Mamu ne - Iyalan Tukur Mamu

Sanarwar ta ce:

"Mun kira ga hukumar yan sandan farin kaya DSS ta dena yi wa Malam Tukur Mamu (Dan Iyan Fika) mawallafin, jaridar Desert Herald wanda suka kama suka tsare tun ranar 6 ga watan Satumba shari'ar 'kafar watsa labarai."

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"DSS a cikin sanarwar manema labarai a ranar Alhamis 8 ga watan Satumba mai taken 'Karin Bayani Kan Mamu' ta yi ikirarin yayin samame da ta kai gidansa da ofishinsa da ke Kaduna ta gano kudade masu yawa na kasashe daban-daban da kayan sojoji.
"Duk da cewa DSS bata fayyace adadin abin da ta kira kudi mai yawa a gida da ofishinsa ba, muna son fayyace cewa kayan sojoji (unifom da hula) na dansa ne, Yahaya Bello, Sojan ruwa wanda ya yi karatu a NDA."

Kara karanta wannan

Soji Sun Ceto 'Yan Matan Chibok 3, Sun Damke Bukar Abatcha, mai Kaiwa 'Yan Ta'adda Makamai

Tukur ne ya rike Bello kuma a gidansa ya girma, sanarwar ta kara da cewa.

Idan za a iya tunawa kimanin makonni biyu da suka gabata, kanin Tukur Mamu, Muhammad Saleh Mamu, ya rasu a yayin wani artabu da yan ta'adda a Zamfara.

DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike

Tunda farko, yan sandan farin kaya na DSS na cigaba da bibiyan wadanda ke da alaka da Tukur Mamu, wanda ya taimaka wurin sulhu da yan bindiga, a yayin da suka kama surukinsa, Abdullahi Mashi, a daren ranar Alhamis.

Daily Trust ta tattaro cewa jami'an yan sandan sirrin sun kuma ziyarci gidan surukin Mamu, Ibrahim Tinja, wanda shima an kama shi an kuma dawo da shi Najeriya tare da mawallafin na Desert Herald a ranar Laraba.

An kama Mamu da sauran iyalansa a filin tashin jirage na Malam Aminu Kano a ranar Laraba bayan an dawo da su daga Misra bisa umurnin hukumomin tattara bayanan sirri na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel