Soji Sun Ceto 'Yan Matan Chibok 3, Sun Damke Bukar Abatcha, mai Kaiwa 'Yan Ta'adda Makamai

Soji Sun Ceto 'Yan Matan Chibok 3, Sun Damke Bukar Abatcha, mai Kaiwa 'Yan Ta'adda Makamai

  • Dakarun sojin Najeriya sun tabbatar da ceto 'yan matan Chibok 3 tare da damke Bukar Abatcha, dillalin makamai dake kai wa 'yan Boko Haram
  • Kamar yadda hedkwatar tsaro ta sanar, an yi nasarar ceto wasu mutum 19 da 'yan Boko Haram suka sace a Borno
  • 'Yan Boko Haram 13 aka damke yayin da wasu 556 da suka hada iyalansu maza da mata tare da yara suka mika wuya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro a ranar Alhamis ta bayyana cewa dakarun Operation Hadin Kai sun cafke mai kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a yankin Asokoro dake babban birnin tarayya na Abuja.

Hakazalika, sun damke wani 'dan kasar ketare dake samarwa 'yan ta'adda makamai kuma dillalin makamai mai suna Abatcha Bukar tare da wasu 'yan ta'adda 13 a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

Nigerian Army
Soji Sun Ceto 'Yan Matan Chibok 3, Sun Damke Bukar Abatcha, mai Kaiwa 'Yan Ta'adda Makamai. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Punch ta rahoto cewa, daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, ya bayyana hakan a zantawar da yayi da manema labarai a Abuja.

Yace an samu nasarar ceto 'yan matan Chibok uku da wasu mutum 19 da aka yi garkuwa da su a cikin lokacin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Danmadami yace:

"Wani da ake zargin bakon haure ne mai samar da makamai ga 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP mai suna Abatcha Bukar ya shiga hannun jami'ai. An kama shi da manyan allurai, katin ATM biyu da kudi N294,520.
“A arewa ta tsakiya, dakarun sojin sun cafke wani mai kaiwa 'yan Boko haram bayanan sirri mai suna Mamuda Usman wanda aka fi sani sa Bado a Asokoro dake babban birnin tarayya.
“Duk a wannan lokacin, dakarun sun halaka 'yan ta'adda 252 yayin da wadanda ake zargi da zama 'yan Boko Haram 556 da iyalansu da suka hada da maza 115, mata 189 da yara 252 suka mika kansu ga dakarun.

Kara karanta wannan

N100,000 Nake Samu Idan Na Kai Harsasai 500: Matashin Mai Kaiwa 'Yan Bindiga Makamai Yace

"Abubuwan da aka samo daga wurinsu sun hada da gurneti 2, AK47 12, babur, kwari da baka 16, kekuna bakwai da wayoyi 10 da sauransu.
“Dakarun sun ceto 'yan mata Chibok uku masu suna Jinkai Yama, Falmata Lawal da Asabe Ali wadanda ke da lamba 3, 20 da 24 na jerin sunayen 'yan matan Chibok din da suka bace. An ceto su a wurare daban-daban da 'ya'yan da suka haifa tare da mutum 19 da aka sace."

'Yan Bindiga Sun Kwashe Matafiya 32 Dake Dawowa Daga Jana'iza a Ondo

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi awon gaba da matafiya 32 a wuraren Ifon dake karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.

Wadanda aka sacen an gano cewa suna dawowa ne daga bikin mutuwa da suka yi a jihar Edo a ranar Asabar lokacin da lamarin ya faru, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tare hanya a Kaduna, suka kashe mutane da dama

Har yanzu ba a tabbatar da cewa ko masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan wadanda suka sacen ba domin biyan kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel