INEC Zata Bude Shafin Daukar Aikin Wucin Gadi Na Zaben 2023

INEC Zata Bude Shafin Daukar Aikin Wucin Gadi Na Zaben 2023

  • Hukumar INEC ta fara shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa, gwamnoni da majalisa na 2023
  • INEC ta sanar da ranar bude shafin daukar ma'aikatan wucin gadi da zasu yi aikin zaben
  • Daga cikin ayyukan da za'a dauka akwai na SPO, PO, APO, RATECHS da RAC

Hukumar gudanar da zaben kasa INEC, a ranar Laraba, ta sanar da fara shirin daukar ma'aikatan da zasu yi aikin zaben kasa da zai gudana a Febrairu da Maris 2023.

INEC zata bude shafin yanar gizo da duk mai son yin aiki ya garzaya ya nema.

Hukumar zaben ta bayyana hakan ne a jawabin da ta fitar a shafinta na Facebook ranar Laraba.

Tace za'a bude shafin ranar Laraba (nan da mako guda) kuma za ta rufe ranar 30 ga Nuwamba, 2022, amma takardar sanarwar, INEC tace ranar 14 ga Disamba za'a rufe.

Kara karanta wannan

2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF

INEC.
INEC Zata Bude Shafin Daukar Aikin Wucin Gadi Na Zaben 2023 Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jawabin:

"Hukumar ta amince da sake amfani da INECPRES na manhaja Andriod kadai da Komfuta."
"Saboda haka an bude shafin ga masu neman aikin wucin gadi (SPO/PO/APO/RATECHS/RAC) illa aikin baturen tattara kuri'u."
"An bude shafin ranar 14 ga Satumba kuma za'a rufe ranar 30 ga Satumba, 2022."

A karshen watan nan za'a kaddamar da ayyukan zaben 2023 wanda ya hada da kamfe da sauran su.

INEC Ta Sanar Da Ranar Wallafa Ta Karshe Na Sunayen Dukkan Yan Takara A Zaben 2023

INEC, za ta saki sunayen dukkan yan takaran da zasu yi musharaka a zaben kasa na shekarar 2023.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja inda ya halarci taron kungiyar Centre for Democracy and Development (CDD).

A cewarsa, hukumar zata saki sunayen yan takaran shugaban kasa, Sanatoci da yan majalisar wakilai ranar 20 ga Satumba, 2022, rahoton Channels.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

Yayinda za'a saki na gwamnoni da majalisar jiha ranar 4 ga Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel