Al’ada Mai Ban Sha’awa: Bidiyoyin Shagalin ‘Lugude’ Na Bikin Ruqayya Bayero, Amarya Da Kawayenta Sun Sha Daka

Al’ada Mai Ban Sha’awa: Bidiyoyin Shagalin ‘Lugude’ Na Bikin Ruqayya Bayero, Amarya Da Kawayenta Sun Sha Daka

  • Ana ci gaba da shagulgulan bikin auren Gimbiya Ruqayya Aminu Bayero da angonta Amir Kibiya a masarautar Kano
  • Cike da nunawa tare da farfado da al'adar mallam Bahaushe tsantsa, an gudanar da shagalin 'Lugude' inda amarya da kawayenta suka sha daka
  • Hotuna da Bidiyoyin wannan shagali mai ban sha'awa sun karade shafukan soshiyal midiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Biki yayi biki a masarautar Kano inda mata ke ta sha’aninsu duk a shirye-shiryen auren Gimbiya Ruqayya Bayero, diyar mai martaba Sarki Aminu Ado Bayero.

Wannan biki ya zo da sabon salo inda aka farfado da al’adun gargajiya na mallama Bahause, an dai shirye wani kasaitaccen taro da aka yiwa lakabi da ‘lugude’.

Bikin Ruqayya Bayero
Al’ada Mai Ban Sha’awa: Bidiyoyin Shagalin ‘Lugude’ Na Bikin Ruqayya Bayero, Amarya Da Kawayenta Sun Sha Daka Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

A cikin bidiyoyin da suka yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano wasu taron mata rike da tabare sannan ga turame a gabansu suna daka tare da wakokin al’ada.

Kara karanta wannan

Yar Manya Jinin Sarauta: Hotuna Da Bidiyoyin Shagalin Kamun Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero

Hakazalika, amarya Ruqayya ta halarci wannan taro inda ta fito a gimbiyarta sak cikin shiga ta gidan sarauta da alkyabba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon da shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram, an gano Gimbiya Ruqayya tare da kawayenta suna daka da waken al’ada irin su ‘Ayye mama-Ayye mama’ wanda akan yiwa amare a lokacin bikinsu.

A gefe kuma, an gano wasu taron mata suna kidin kwarya irin na zamanin iyaye da kakkani a kasar Hausa.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Yar Manya Jinin Sarauta: Hotuna Da Bidiyoyin Shagalin Kamun Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero

A baya mun ji cewa shagali ya kankama a masarautar Kano na auren Gimbiya Ruqayya Aminu Bayero da angwanta Amir Kibiya.

Tuni kyawawan bidiyoyi da hotunan shagalin kamun bikin suka yadu a shafukan soshiyal midiya.

A cikin hotunan da shafin shahararriyar MC nan ta arewa surykmata ta wallafa a Instagram, an gano amarya tare da mahaifinta da kuma sauran dangi cikin farin ciki.

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

Asali: Legit.ng

Online view pixel