Hotunan Mayakan Kasar Waje Masu Alaka Da Boko Haram Da Aka Kama A Benue

Hotunan Mayakan Kasar Waje Masu Alaka Da Boko Haram Da Aka Kama A Benue

  • Hukumar tsaro ta Jihar Benue, BSCVG, ta kama wasu mutane da ake zargin mayakan Ambazoniya ne masu alaka da kungiyar Boko Haram
  • Laftanant Kanal Paul Hemba (mai ritaya), mashawarci na musamman ga gwamnan Benue kan tsaro ya tabbatar da kama wadanda ake zargin
  • Hemba ya ce yayin bincike an gano suna dauke da bindigu, layyu, makaman kemical da wasu muggan abubuwa kuma an mika su ga yan sanda

Jihar Benue - Jami'an tsaro na jihar Benue, BSCVG, sun kama wasu mutane biyar da ake zargin mayakan kungiyar Ambazonia ne a Jihar Benue, The Punch ta rahoto.

Mashawarci na musamman kan tsaro, Laftanant Kanal Paul Hemba (mai ritaya), cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce an kama wadanda ake zargin ne masu alaka da Boko Haram a ranar Litinin a kusa da shataletalen Jato Aka.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ‘Yan fanshi da Barayi Sun sace Wayoyi 76 da Kayan kusan N5m

Wadanda ake zargi
An Kama Wasu Mayakan Kasar Waje 5 Masu Alaka Da Boko Haram A Benue. Hoto: @thesunnigeria.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An bayyana sunanyen wadanda ake zargin kamar haka: Stanley Vincent, mai shekara 25; David Ojong, Ronado Njeke, mai shekara 42; Emmanuel Ngum da Samuel Obem, mai shekara 26, rahoton The Sun.

Daya daga cikin wadanda ake zargin ya magantu

Mashawarcin gwamnan na musamman ya ce Stanley ya ce mai gidansa ne ya umurci ya su yi rakiya zuwa Kamaru, ya kara da cewa sun fara zarginsa ne bayan gano baya dauke da katin shaida.

Wani sashi na sanarwar:

"A ranar 22 ga watan Agusta, misalin karfe 3 na rana a shataletalen Jato Aka, kusa da mashaya na Dzoho Aondofa, karamar hukumar Kwande, BSCVG sun kama wasu mutum biyar da ake zargin mayakan Ambazonia ne ake zargin suna da alaka da Boko Haram da masu neman kafa Jamhuriyar Ambazonia tsawon shekara biyar.

Kara karanta wannan

Ni Na Kashe Sheik Goni Aisami, Jami'in Sojan Da Aka Kama Ya Laburtawa Yan Sanda

"Karin binciken da aka yi ya sa an gano makaman kemical, kayan sojoji, layyu da bindigu tare da yan Amazoniyan wanda suka ce sun shafe wata shida a Agogo Hotel, mallakar wani Dooorun Agogo."

An mika wadanda ake zargin hannun yan sanda da ke Adikpo, hedkwatar karamar hukumar Kwande.

Mashawarcin na tsaro ya ce laifuka da ake aikatawa na fashi da garkuwa cikin watanni shida a garin ba zai rasa nasaba da wadanda ake zargin ba.

An Kama Sojoji 2 Kan Laifin Kashe Babban Malamin Islama, Sheikh Goni Aisami, Tare Da Sace Motarsa A Yobe

A wani rahoton, rundunar yan sandan Najeriya a Yobe ta kama sojoji da ake zargi da hannu a kisar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami wanda aka kashe ranar Juma'a misalin ƙarfe 9 na dare a hanyarsa ta komawa Gashua daga Kano.

Majiyoyi da dama daga garin sunyi zargin cewa sojojin sun kashe malamin ne bayan ya rage musu hanya daga shingen sojoji a Nguru zuwa Jaji-maji, wani gari da ke karamar hukumar Karasuwa na Jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel