Soyayyar Gaskiya: Bidiyon Auren Kyakkyawar Doguwar Amarya da Wadan Angonta ya Janyo Cece-kuce

Soyayyar Gaskiya: Bidiyon Auren Kyakkyawar Doguwar Amarya da Wadan Angonta ya Janyo Cece-kuce

  • Wani bidiyo dake ta yawo ya nuna doguwar budurwa tana auren wadan namiji a yayin da suke liyafar cin abinci ta aurensu
  • Bidiyon ya janyo martani kala-kala daga ma'abota amfani da yanar gizo inda wasu suke cewa a bar su su ci amarcinsu
  • Wasu kuwa sun dinga tantama kan cewa amarya bata cikin farin ciki tunda an gan ta zaune yayin da angon ke tikar rawansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bidiyon wata doguwar amarya tare da gajeren angonta ya janyo cece-kuce mai yawa a kafafen sada zumuntar zamani.

Bidiyon ya nuna lokacin da angon gajere ya shiga wurin liyafar tare da amaryarsa, wacce ko kusa ba tsawonsu daya ba.

Gajeren Ango
Soyayyar Gaskiya: Bidiyon Auren Kyakyawar Doguwar Amarya da Wadan Angonta ya Janyo Cece-kuce. Hoto daga TikTok/@maan....yg
Asali: UGC

Soyayyar gaskiya ce

A gajeren bidiyon da aka gani a Instagram, an ga angon yana ta tikar rawa shi kadai a wurin liyafar yayin da matarsa take zaune kuma tana magana da wani.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuni dai bidiyon ya janyo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, inda wasu ke musun cewa alakar da ta hada su soyayya ce.

Wasu kuwa sun dinga tantama inda suka ce matar bata farin ciki tunda take zaune a lokacin da angonta ke kwasar rawa.

Kalla bidiyon:

Jama'a sun yi martani

@josephtony_01 yace:

"Wannan farin gayen dake ta rawa gaskiya zundensu yake yi."

@jhane_the yace:

"Sai a yau rayuwar da nake yi babu aure ta bata min rai."

@iamdx2 yace:

"Kana kasa, sanyi na kara zuwa."

@cydmnd yace:

"Abun dariya... Matar nan bata farin ciki."

@therapist_roundtable yace:

"Saboda kun ga mutum biyu a cikin kayan aure ana daura musu aure, baya bayyana soyayya. Shagalin aure ba soyayya ta gaskiya bace. Rayuwa bayan auren ita ce lokacin da ake gane gaskiyar soyayya."

Kara karanta wannan

Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

Hotuna da Bidiyon kyawawan 'ya'ya matan Yariman Bakura a Shagalin Auren 'Dan uwansu

A wani labari na daban, kyawawan hotunan 'ya'ya matan Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura sun matukar birge jama'a a soshiyal midiya.

Kamar yadda fashionseriesng ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga zuka-zukan 'yan matan hudu jere reras gwani sha'awa.

Suna sanye da kaya masu kusan launi daya yayin da suka sha kwalliya irin ta zamani mai matukar birgewa da aji irin na 'ya'yan masu hannu da shuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel