Akanta Janar da Aka Dakatar, Ahmed Idris Yana Neman Yin Sulhu da Lauyoyin EFCC

Akanta Janar da Aka Dakatar, Ahmed Idris Yana Neman Yin Sulhu da Lauyoyin EFCC

  • Ahmed Idris zai so hukumar EFCC ta janye karar da ta shigar da su, sai su sasanta a tsakaninsu
  • Lauyan da ya kai kara, Rotimi Jacobs ya fadawa Alkali cewa Mista Idris yana neman ya gana da shi
  • A karshe hakan ba ta yiwu ba saboda Lauyoyin tsohon Akantan kasar sun ce ba su san da batun ba

Abuja - Ahmed Idris wanda aka dakatar daga matsayin babban akawun gwamnatin tarayya, yana neman ya yi sulhu da hukumar EFCC da ke kararsa.

Rahoton The Cable na ranar Laraba, 10 ga watan Agusta 2022, yace wanda ake kara ya fara shirin ganin yadda za a janye tuhumar da ake yi masu a kotu.

Da aka koma kotu a jiya da rana, sai Lauyan da ya tsayawa EFCC, Rotimi Jacobs ya shaidawa Alkali, Idris da sauran wanda ake zargi sun tuntube shi.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

Rotimi Jacobs yake cewa wadanda ake karar suna neman haduwa da shi ne saboda a janye karar.

Abin da Lauya ya fadawa kotu

“Mai shari’a, wadanda ake tuhuma sun aiko mani da wani mutum, suna so mu sasanta, kuma suna neman ganawa da ni,”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Amma amsar da na ba su ita ce, ba zan iya haduwa da su ba a gaban lauyoyinsu ba.”
Ahmed Idris
Ahmed Idris a kujerar AoGF Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Saboda yanayin aikinmu, dole ne muyi komai keke-da-keke cikin gaskiya.”

- Rotimi Jacobs

Ayi komai a gaban Lauyoyi

Vanguard ta rahoto Jacobs yana cewa tun da sashe na 270 na dokar shari’a ta kasa ta amince da irin wannan tsari, ya bukaci Idris su zo da layoyinsu.

Shi ma Lauyan na EFCC ya yi alkawarin gayyato masu bincike daga bangarensa wajen ganawar. A karshe dai har zuwa jiya, hakan ba ta yiwu ba.

Kara karanta wannan

Azabar Ta Yi Yawa: Ma’aurata Sun Maka Makwabcinsu Da Zakaransa A Kotu, Hotunan Sun Yadu

Jacobs yake cewa daga baya Lauyoyin Idris sun same shi a ofishinsa, inda suka nuna fushinsu saboda an ware su, a dalilin hakan aka fasa wannan zama.

Sulhu a wajen kotu

A kotu akwai tsarin da ake bi ta yadda za a cin ma matsaya tsakanin wanda ake kara da bangaren wanda ya shigar da kara, ta yadda za a daina shari’ar.

Kotu ta kan amince da wannan tsari idan har Lauyoyi sun gamsu maganar ta bar teburin Alkali. A irin wannan, kowa bai samu cikakken abin da yake so.

Caccakar Tinubu a kan lafiyarsa wauta ce

Dazu aka ji labari Dr. Chimaroke Nnamani yi Allah-wadai da masu sukar Bola Tinubu, duk da sabaninsu, yace ba a taba yin ‘dan siyasa irin Tinubu ba.

Sanatan Enugu ya bada shawarwari na musamman ga Bola Tinubu game da mai dakinsa da masu kamfe da halin lafiyar ‘dan takaran na 2023.

Kara karanta wannan

Mafi tsufa a raye: An gano wani tsoho dan Najeriya mai shekaru 126 a raye kuma da karfinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel