Sunaye: Yan Ta'adda Sun Sake Sako Mutum 7 Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa Da Taimakon Sheikh Gumi

Sunaye: Yan Ta'adda Sun Sake Sako Mutum 7 Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa Da Taimakon Sheikh Gumi

  • Yan ta'adda da suka kai wa fasinjojin jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna hari a ranar 28 ga watan Maris sun sake sako mutum bakwai
  • Wadanda aka sako din sun kunshi magidanci, Abubakar Garba Idris da matarsa da yaransa ciki har da yarinya yar shekara daya da rabi
  • Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna ya tabbatar da sakinsu yana mai cewa an yi nasarar sakinsu ne bayan Sheikh Ahmad Gumi ya shiga tsakani

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yan ta'addan da suka kai hari a jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun sake sako mutum bakwai da suka hada da yan gida daya da mace.

Gumi Da Wasu Fasinjojin Jirgin Kasa Da Aka Sako.
Yan Ta'adda Sun Sake Sako Mutum 7 Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa, An Bayyana Sunayensu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sunayen wadanda aka sako din sune Abubakar Idris Garba, matarsa, Maryam Abubakar Bobo, babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba, mai shekara 10.

Saura sun hada da Fatima Abubakar Garba, mai shekara 7, Imran Abubakar Garba, mai shekara 5 da karamin cikinsu Zainab Abubakar Garba mai shekara daya da rabi.

Fasinjojin Jirgin Kasa.
Yan Ta'adda Sun Sake Sako Mutum 7 Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa, An Bayyana Sunayensu. Hoto: Desert Herald.
Asali: Twitter

Abubakar Garba Idris, ma'aikacin hukumar majalisar tarayya, da ne ga tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano da Benue.

An kuma saki wata mata mai shekaru 60, wata Hajiya Aisha Hassan, wanda aka ce an sako ta ne saboda rashin lafiya da ta ke fama da shi, The Cable ta rahoto.

Sheikh Ahmad Gumi ya taimaka wurin ganin an sako mutanen bakwai

Duk da cewa Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald kuma mashawarci a bangaren kafar watsa labarai ga Sheikh Ahmad Gumi, ya janye daga cikin masu sassanci, ya tabbatar da sakin mutanen bakwai ga manema labarai a Kaduna.

Mamu ya ce an saki mutanen bakwai ne bayan shiga tsakani da mai gidansa, Sheikh Gumi ya yi.

A watan Yuni, an sako mutum 11 cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su.

A watan Yuli, an sako mutum bakwai cikin wadanda aka sace din - Sadiq, dan Ango Abdullahi shugaban kungiyar dattawan arewa, NEF, yana cikin mutanen bakwai.

Dukan Fasinjojin Jirgin Kasa: Duk Munafukai Ne Masu Allah Wadai A Soshiyal Midiya, Naziru Sarkin Waka

A wani rahoton, shahararren mawakin masana’antar Kannywood Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Naziru Sarkin waka ya yi martani kan bayyanar bidiyon yan ta’adda yayin da suke azabtar da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Sarkin waka ya ce duk munafirci ne ke sa mutane zuwa shafukan soshiyal midiya suna dora bidiyon tare da yin Allah wadai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel