Dukan Fasinjojin Jirgin Kasa: Duk Munafukai Ne Masu Allah Wadai A Soshiyal Midiya, Naziru Sarkin Waka

Dukan Fasinjojin Jirgin Kasa: Duk Munafukai Ne Masu Allah Wadai A Soshiyal Midiya, Naziru Sarkin Waka

  • Mawakin masana'antar Kannywood, Naziru Ahmad, ya caccaki masu yin Allah wadai da bidiyon dukan fasinjojin jirgin kasa a soshiyal midiya
  • Naziru sarkin waka ya zargi mutane da sako munafirci a lamarin domin a cewarsa ba a tunawa da fasinjojin sai an turo bidiyonsu ana azabtar da su
  • Jarumin fim din ya shawarci mutane da su koma ga Allah don neman mafita domin zagin gwamnati ba shine hanyar magance abun ba a yanzu

Shahararren mawakin masana’antar Kannywood Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Naziru Sarkin waka ya yi martani kan bayyanar bidiyon yan ta’adda yayin da suke azabtar da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Sarkin waka ya ce duk munafirci ne ke sa mutane zuwa shafukan soshiyal midiya suna dora bidiyon tare da yin Allah wadai.

Ya kuma ce yin tir da gwamnati a kan wannan matsala ta rashin tsaro ba shine mafita ba domin shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran gwamnonin arewa duk sun fito sun bayyana cewa sun yi iya bakin kokarinsu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mu muka tallata Buhari, dole mu fito mu fadi gaskiya, Naburaska ya cashe gwamnati

Naziru da fasinjojin jirgin kasa
Dukan Fasinjojin Jirgin Kasa: Duk Munafukai Ne Masu Allah Wadai A Soshiyal Midiya, Naziru Sarkin Waka Hoto: sarkin_wakar_san_kano
Asali: Instagram

Naziru ya ci gaba da cewa don mutum ya fito shafukan sadarwa ya ce ya kasa bacci ko ya kasa cin abinci duk bashi ke nuna yana tausayawa mutanen da lamarin ya ritsa da su har cikin ransa ba. Babban abun da za a yi shine a taya wadannan mutane da addu’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kamata a zauna a nemo mafita domin wannan al'amari na ta'addanci Musulmai ya fi ritsawa da su.

Ya ce:

“Dan Allah mutane me yasa bama tunawa da yanayin da wadannan mutane da ibtila’in jirgin kasan nan ya ritsa da su sai an turo bidiyonsu ana azabtar da su ko suna cikin wani yanayi, anya ko addu’a muna yi masu kuwa?, anya wadannan rubuce-rubucen da muke yi a soshiyal midiya na kasa bacci, wannan ya yi Allah ya isa kuna ganin shine mafita?

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhari Da Yan Ta'adda Suka Fitar

“Toh karya muke munafirci ya fi yawa a cikin al’amuran mutane da mu dukka. Dalili, kwana biyu ne uku da an yi mun manta amma da an wullo bidiyonsu mun iya mu sako gwamnati a gaba muna zagi. Toh in yi maku a takaice, idan mutane ne mu masu ganewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari duk bayanin da zai yi yau shekaru nawa yana yi iya abun da zai iya ya riga ya yi. Gwamna Nasir el-Rufai ya fada abun da za su iya sun yi. Zulum muna kallonsa a kan titi yana yawo yanda ka san shine jami’in tsaron.
“Mun wayi gari sai an wullo bidiyon mutanen nan sannan za mu ji tausayinsu. Duk kwana dari da wani abu da suka yi bamu ware wata daya mu zauna tun farko mu ce kullun akwai gurin addu’a koda da safe ne. anya mun yarda cewa Allah ne zai kawo karshen wannan al’amari?”

Kara karanta wannan

‘Ya Da Uwa Sun Fashe Da Kukan Kewar Rabuwa Da Juna A Wajen Liyafar Bikin Diyar, Bidiyon Ya Taba Zukata

Kalli cikakken bidiyon a kasa:

Gwamnatin Nan Ta Gaza Mana, In Ji Jaruma Maryam Booth Kan Bidiyon Dukan Fasinjojin Kaduna-Abuja

A gefe guda, mun kawo a baya cewa fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Booth ta bi sahun takwarorinta wajen yin tir da sabon bidiyon da yan ta’adda suka saki inda suke jibgan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Maryam Booth a wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram ta bayyana cewa lallai wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gazawa al’ummanta.

Jarumar ta bayyana hakan ne a rubuce a kasan bidiyon da miyagun suka saki inda suke ta dukan fasinjojin wadanda suka yi garkuwa da su tun a ranar 28 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel