Kamfanin Whatsapp Ta Yiwa Manhajjanta Karin Ka’aidojin Boye Sirri Guda 3

Kamfanin Whatsapp Ta Yiwa Manhajjanta Karin Ka’aidojin Boye Sirri Guda 3

  • WhatsApp zata gabatar da sabbin ka’idojin boye sirri guda uku a cikin manhajatta don kare sakonnin mutane
  • Kamfanin Whatsapp ta ce manhajjatar ta fito da sabon tsarin da zai hana mutane daukan hoton alli 'screenshot' din hoto da ka tura ba tare da izinin ka ba
  • Mai Kamfanin Whatsapp Mark Zuckerberg ya dau alkawarin ba da kariya ga sirrin masu amfani da WhatsApp

WhatsApp zata gabatar da sabbin ka’idojin boye sirri guda uku a cikin manhajatta don kare sakonnin mutane, kamfanin ta sanar da haka a ranar Talata. Rahoton Legit.NG

A cikin wata sako da fitar shafin ta na yanar gizon, whatsapp wanda mallakar kamfanin Meta ce ta bayyana cewa sabon fasalin zai baiwa masu amfani da shi iko akan tattaunawar su akan manhajjar.

WhatsApp zai ba mutane damar fita daga tattaunawar rukuni wato ‘group chat’ ba tare da sanin membobin da ke cikin irin waɗannan rukunin ba.

MARKY
Kamfanin Whatsapp Ta Yiwa Manhajjanta Karin Ka’aidojin Boye Sirri Guda 3 FOTO Mark Zukerberg
Asali: Facebook

Da zarar kafita daga rukunin tattaunawa ‘group chat’ shugaban rukunin wato ‘admin’ kadai zai san wani ya fita amma sauran baza su sani ba. Karshen wannan watan zai fara aiki kamar yadda Premium Times ta rawaito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakanan zai hana yin hoton allo akan saƙonnin ‘Screenshot’ da aka saita don gogewa bayan an karanta ko kallo sau ɗaya.

Ka’idar boye siiri ta karshe shine za ta ba masu amfani damar sarrafa waɗanda za su iya ganin su lokacin da suke kan layi da wanda basa son su gan su akan layi, fasalin da zai fito a cikin wannan watan.

Babban Jami'in Meta, Mark Zuckerberg ya rubuta game da sabbin abubuwan a shafinsa na Facebook kuma ya yi alkawarin ba da kariya ga sirrin masu amfani da WhatsApp.

Biyubabu: Lawan Da Akpabio Ba Sa Cikin Yan Takarar Senata, INEC

A wani labari kuma, Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan matsayin ‘yan takarar senata a Yobe ta Arewa da Godswill Akpabio a matsayin dan takarar senata a Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba. Rahoton LEADERSHIP

Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan matsayin ‘yan takarar senata a Yobe ta Arewa da Godswill Akpabio a matsayin dan takarar senata a Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba. Rahoton LEADERSHIP

Asali: Legit.ng

Online view pixel