Rikicin PDP: Atiku da Gwamna Wike Sun Cimma Matsayar Kafa Kwamitin Mutum 14

Rikicin PDP: Atiku da Gwamna Wike Sun Cimma Matsayar Kafa Kwamitin Mutum 14

  • Ga dukkan alamu jam'iyyar PDP ta fara nemo bakin zaren game da rikicin ɗan takararta, Atiku Abubakar da gwamna Wike
  • Wani ƙusa a jam'iyyar ya tabbatar da cewa ganawar mutanen biyu ta yi armashi har sun fara lalubo hanyar sasantawa
  • Jiga-jigan biyu sun amince da kafa sabon kwamitin mutum 14 da zai zauna ya tattauna, neman shawari kana ya bada shawarin da kowa zai na'am da su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Sakamakon taro tsakanin ɗan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, da gwamna Nyesom Wike na Ribas, an kafa wani kwamitin mutum 14 da zai tattauna kuma ya ba da shawarwari wanda jiga-jigan biyu zasu diba.

Wata babbar majiya mai alaƙa da cigaban ce ta sanar da jaridar Vanguard ranar Lahadi cewa ba'a bayyana wa duniya kwamitin bane saboda har yanzu akwai mambobin kwamitin da ba'a sanar da su ba.

Kara karanta wannan

Kuri'ar Gamsuwa: PDP Ta Aminta Da Salon Jagorancin Ayu Duk Da Rikicin Jam'iyyar

Gwamna Wike tare da Atiku.
Rikicin PDP: Atiku da Gwamna Wike Sun Cimma Matsayar Kafa Kwamitin Mutum 14 Hoto: thecableng
Asali: UGC

Majiyar wacce ta yi jawabi da sharaɗin boye bayananta saboda wasu dalilai ta ce kwamitin zai fara fara aikin da aka ɗora masa nan take.

Babbar jam'iyyar hamayya watau PDP ta afƙa cikin rikici tun lokacin da Atiku Abubakar ya zaɓi gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin ɗan takarar mataimaki a zaɓen 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wannan zaɓin ya saɓa wa tunanin wasu masu faɗa aji na PDP da ke tunankn Wike ya fi dacewa da matsayin bayan ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani wanda aka ayyana Atiku a matsayin ɗan takara.

Mako biyu da suke wuce, Atiku da gwamna Wike sun yi musayar zafafan kalamai kan zaɓen mataimaki, lamarin da ya sa kwamitin amintattu suka shiga tsakani.

"Mun samu cigaba cikin awanni 24 da suke wuce bayan ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da gwamna Nyesom Wike sun gana. Taron ya ba maƙiyan PDP mamaki," inji majiyar.

Kara karanta wannan

An Fallasa Wani Shirin Gwamna Wike, Da Yuwuwar Zai Yaƙi Atiku Ya Koma Bayan Wannan Ɗan Takarar a 2023

Shin wani bangare ya gindaya sharudda ne?

Da aka tambaye shi ko an gindaya wasu sharuɗɗa a zaman, majiyar ta ƙara da cewa:

"Zancen kafa wasu sharuɗɗa be taso ba lokacin da mutanen biyu suka jingine sabanin da ke tsakanin su, suka yi magana da juna. Duk shawarwarin da wannan kwamiti ya bayar za'a duba su kuma a ɗauki mataki."

Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan rikicin, kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya bayyana kwarin guiwar cewa nan ba da jimawa ba za'a kawo ƙarshen komai.

A wani labarin, tun farko kun ji cewa Atiku Abubakar da Gwamna Wike sun gana da juna a gidan wani tsohon minista a Abuja

A karon farko tun bayan zaɓen fidda gwani, Atiku Abubakar da gwamna Wike sun gana a birnin tarayya Abuja.

Wata majiya ta ce taron ya yi armashi sosai kuma akwai wasu taruka da zasu biyo baya a kwanaki kaɗan masu zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

Asali: Legit.ng

Online view pixel