Bidiyo Da Hotunan Budan Kan Yacine Sheriff, An Mika Ta A Hannun Surukarta, Turai Yar’adua

Bidiyo Da Hotunan Budan Kan Yacine Sheriff, An Mika Ta A Hannun Surukarta, Turai Yar’adua

  • Daga karshe an rufe shagulgulan bikin Yacine Sheriff da angonta dan tsohon shugaban kasa Shehu Yar'adua
  • An gudanar da budan kan amarya inda aka mika Yacine a hannun surukarta, Hajiya Turai Yar'adua
  • Tun a ranar 23 ga watan Yuli ne aka daura auren Shehu Yar’adua da amaryarsa Yacine Muhammad Sheriff a Maiduguri, jihar Borno

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

An gudanar da shagalin biki na karshe wato ‘budan kan amarya’ Yacine Sheriff wacce aka daura aurenta da angonta Shehu Umaru Yar’adua.

Tun a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli ne aka kulla aure tsakanin dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Shehu Yar’adua da amaryarsa Yacine Muhammad Sheriff amma sai aka ci gaba da shagulgulan biki.

Kamar yadda yake bisa al’adar mutanen yankin arewacin Najeriya a kan rufe taron biki ne da budan wanda dangin ango kan yi bayan an kai amarya gidan mijinta.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyo: Dankareriyar daham din da Fatima Shettima ta saka wurin wushe-wushe ya dauka hankali

Turai Yar'adua
Bidiyo Da Hotunan Budan Kan Yacine Sheriff, An Mika Ta A Hannun Surukarta, Turai Yar’adua Hoto: theweddingstreet_ng
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da shafin theweddingstreet_ng ya wallafa a Instagram, an gano inda yan uwan amarya suka shigo da ita lullube cikin mayafi sannan aka gabatar da ita a gaban surukarta kuma uwargidar tsohon shugaban kasa Umaru Yar’adua, Hajiya Turai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai Turai Yar’adua ta karbe ta hannu bibbiyu tare da rungume ta sannan daga bisani wata yar’uwarta ta yane mayafin da ke kan amaryar.

Bayan nan sai aka sada amarya Yacine da dakinta inda ta dunga sharar kwalla da ke zubowa daga idanunta wanda ke nuna alamun kewar yan’uwa.

Kalli bidiyon a kasa:

Hotuna Da Bidiyoyin Ali Modu Sheriff Yana Nasiha Ga Diyar Danuwansa, Yacine da angonta Shehu Yar’adua

A baya mun kawo cewa kamar yadda yake bisa al’ada a kan zaunar da ma’aurata sannan a yi masu nasiha tare da wayar da kansu kan wannan sabuwar rayuwa da za su shiga.

Kara karanta wannan

Shagalin Biki Na Manya: Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Daga ‘Kunshin’ Fatima Shettima

Hakan ce ta kasance a bangaren kawun amarya kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Mosu Sheriff wanda ya zaunar da diyar dan uwan nasa da mijinta Shehu ya kuma hada su ya yi masu nasiha mai ratsa zuciya.

A wani bidiyo da shafin weddingpostng ya wallafa a Instagram, an gano amarya Yacine da angon nata durkushe a gaban kawun nata yayin da yake masu fada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel