Lauya ya Kai Tinubu Gaban Kotu, Ana Neman Hana Sa Takara Saboda Dauko Musulmi

Lauya ya Kai Tinubu Gaban Kotu, Ana Neman Hana Sa Takara Saboda Dauko Musulmi

  • Osigwe Momoh wanda kwararren Lauya ne da yake aiki a Abuja, ya shigar da karar jam’iyyar APC
  • Lauyan yana ganin tsaida Sanata Kashim Shettima da Bola Tinubu ya yi, ya sabawa tsarin mulkin Najeriya
  • Momoh ya bukaci kotu ta wargaza takarar Tinubu da APC a zaben 2023 saboda tikitin Musulmi-Musulmi

Abuja - Wani Lauya mai suna Barista Osigwe Momoh ya shigar da karar jam’iyyar APC mai mulki, da ‘dan takararta, Bola Ahmed Tinubu, kara a kotu.

Jaridar nan ta The Cable ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 25 ga watan Yuli, 2022 cewa Osigwe Momoh yana kalubalantar takarar Kashim Shettima.

Bola Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ne a matsayin abokin takararsa, dukkansu ‘yan takaran biyu Musulmai ne.

Wannan Lauya ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1188/2022 a babban kotun tarayya da ke zama a Abuja, yana rokon a hana Tinubu shiga takara.

Kara karanta wannan

Sha'awar cancanta ne Yasa muke Goyon bayan Tinubu maimakon Peter Obi - Matasan Ibo

An saba dokar kasa

Lauyan yake cewa abinda jam’iyyar APC tayi na dauko musulmi a matsayin abokin takarar Tinubu a zaben 2023, ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Momoh, sashen tsarin mulki ya wajabtawa jam’iyyun siyasa dauko ‘dan takarar shugaban kasa da na mataimakinsa daga wurare dabam-dabam.

Bola Tinubu/Kashim Shettima
Bola Tinubu tare da Kashim Shettima Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Channels ta rahoto Lauyan yana cewa ya kamata abokin takarar Bola Tinubu ya zama Kirista daga wani sashe na kasar nan tun da shi din Musulmi ne.

Wannan Lauya da ke aiki a Abuja, ya kuma roki Alkali ya yi amfani da sassa na 14 (1) & (3), 15 da na 224(a) na tsarin mulki, ya ruguza takaran jam'iyyar APC.

A cewar Momoh, idan aka duba bangare na II na kundin tsarin mulkin Najeriya, za a fahimci babu yadda Musulmai biyu za su tsaya takara a kan tikiti daya.

Kara karanta wannan

Manyan Kudu sun yi watsi da APC, Tinubu, sun ki halartar bikin kaddamar da Shettima

Bisa wannan dalili da Lauyan yake ikirari, ya bukaci kotu ta hana jam’iyyar APC da Tinubu yin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa da za a shirya a 2023.

Rahoton ya ce har zuwa yanzu dai ba a iya sa ranar da Alkali zai saurari wannan kara ba tukuna.

Abin da doka tace - Machika esq

Mun tuntubi wani Lauya, Abdullahi Machika, wanda ya bayyana mana cewa dokar kasa ba ta amince a maida wani bangare saniyar ware a Najeriya ba.

Machika wanda masanin shari'a ne, ya fadawa Legit.ng Hausa cewa kundin tsarin mulki ya yi umarni da a rika damawa da kowa wajen kafa gwamnati.

Wannan lauya yake cewa doka ba ta halastawa wani bangare yin baba-kere a kan mukamai ba, kuma an wajabtawa jam'iyyun siyasa bin wannan dokar.

NNPP ta ce Buhari ya sauka

Dazu aka ji rahoto Jam’iyyar NNPP ta bada shawarar a tunbuke Muhammadu Buhari idan ya ki rubuta takardar murabus daga kujerarsa ta shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

Shugaban NNPP a Katsina yace Gwamnatin APC ta gagara cika alkawarin da ta dauka, tace ‘yan bindiga sun kashe mutum kimanin 50, 000 a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel