Dakarun Najeriya sun samu sa’a, sun bindige ‘Dan bindigan da ya addabi Kaduna

Dakarun Najeriya sun samu sa’a, sun bindige ‘Dan bindigan da ya addabi Kaduna

  • A makon nan Rundunar sojojin Najeriya suka yi artaba da wasu gungun ‘Yan bindiga a Kaduna
  • Dakarun sun yi ta-maza, sun hallaka mutum daya wanda aka gano cewa hatsabibin ‘Dan bindiga ne
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar da jawabi, ya tabbatar da haka

Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya da ke yakar ta’addanci a jihar Kaduna, sun yi nasarar harbe wani hatsabibin ‘dan bindiga da ya yi suna a yankin Chikun.

Kamar yadda Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar da jawabi a jiya, an yi kicibis da ‘dan bindigan ne a wajen Kidunu.

Mista Samuel Aruwan ya ce an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da miyagun ‘yan bindigan.

Daily Trust ta ce Kwamishinan ya fitar da wannan jawabi ne a ranar Talata, 19 ga watan Yuli 2022, aka tabbatar da nasararori da jami’an tsaron suka samu.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga Bayan Musayar Wuta, Sun Kwato Bindigun AK-47 Da Babura

Bayan hallaka mutum daya, sojojin Najeriyan sun samu makamai da kuma wasu kayan surkule a hannun miyagun ‘yan bindigan, kamar yadda jawabin ya tabbatar.

Jawabin Kwamishinan Kaduna

“A cikin sa’o’i 48 da suka shude, jami’an tsaro sun dakile wasu ‘yan bindiga dadi a Kidudu da ke yankin babban titin Eastern By-Pass, a Chikun.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dakarun Najeriya
Sojojin Najeriya a yankin Borno Hoto: @NigerianArmy
Asali: Facebook

“Bayan an yi ta musayar wuta, an ga karshen wani ‘dan bindiga, wanda daga baya aka gane cewa wani hatsabibi ne da ya addabi wannan yanki.”
“An gano bindigogin AK-47 biyu, tare da wasu kayan siddabaru, da wayar salula da babura biyu.”

'Yan bindiga za su yi ta'adi

Jaridar ta ce Kwamishinan ya kuma shaida cewa gwamnatin Kaduna ta samu bayanan sirri da ke nuna ‘yan bindiga su na niyyar kai hare-hare a wasu wurare.

Aruwan ya sanar da jama’a cewa gwamnatin jihar ta na aiki da jami’an tsaro dare da rana domin ganin ta taimaka masu da bayanai da abubuwan da ake bukata.

Kara karanta wannan

Nasara: Tsageru sun sha ragargaza yayin da suka farmaki sansanin soji a jihar Neja

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta na ba jami’an tsaron gudumuwar bayanai da kayan aiki da nufin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a jihar.

Buhari a fadar Sarki

Ku na da labari cewa saƙon Abdulmumini Kabir Usman ga Muhamamadu Buhari shi ne a kammala manyan ayyukan cigaban da Gwamnatin Tarayya ta fara.

Mai martaba Sarkin Katsina yana son ganin mutane sun amfana da gwamnati mai-ci wanda za ta sauka a 2023, ta hanyar kawo ayyuka da samar da tsaro a kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel