Kebbi: Bagudu Butulu ne, Yana Yakar Wadanda Suka Masa Halacci, Shugaban APC

Kebbi: Bagudu Butulu ne, Yana Yakar Wadanda Suka Masa Halacci, Shugaban APC

  • Abdullah Muhammad, shugban APC tsagin Aliero a jihar Kebbi, ya kwatanta gwamna Bagudu da 'dan tsako, ci ka goge baki
  • Yace duk wadanda suka tsaya tsayin daka suka tabbatar gwamnan ya hau kujera da yake, ya yi watsi dasu tare da yi musu butulci a jihar
  • Yace gwamnan ya kakaba musu 'yan tara ne a jihar ba tare da ya bari an yi zabukan fidda gwani ba, kuma zaman Abujansa ya fi zama Kebbi yawa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kebbi - Abdullahi Muhammad, shugaban wani tsagi na APC a jihar Kebbi, ya zargi gwamnan jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, da haddasa rikici a jam'iyyar reshen jihar ta hanyar yakar wadanda suka kafa ta.

Muhammad, tsohon kwamishina a jihar, ya bayyana wannan zargin ne yayin zantawa da Trust TV a wani shirin siyasa.

Kara karanta wannan

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

Gwamna Atiku Bagudu
Kebbi: Bagudu Butulu ne, Yana Yakar Wadanda Suka Masa Halacci, Shugaban APC. Hoto daga daily_tyrust
Asali: Twitter

Yayin martani kan rikicin jam'iyyar inda 'ya'yan jam'iyyar ke ta sauya sheka zuwa jam'iyyun adawa, Muhammad yace duk wani kokarin sasanta sassan jam'iyyar na jihar da ake yi, ya gagara inda yace gwamnan jihar na kokarin watsi da wadanda suka taimaka masa ya kai ga kujerrarsa tun farko.

Yace, "Matsalar Kebbi a bayyane take kuma ta daban ce. Wadanda na lissafo, Sanata Muhammad Aleiro, tsohon gwamna kuma tsohon ministan FCT kuma yanzu Sanata; sun hada da babban sakataren tarayya na NDC wanda yanzu sanata ne kuma yake rike da mukamin shugaban jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An yi watsi da wadannan mutanen, an ware su tare da duk wadanda suka taimaka musu wurin kafa jam'iyyar har ta kai inda take.
"A gaskiya babu gaskiya kuma babu mayar da hankali a jam'iyyar a jihar."

Muhammad, wanda shugaban jam'iyyar ne a tsagin da Aleiro yake, yace jam'iyyar bata yi zabukan fidda gwani na gaskiya a jihar ba inda ya kara da cewa gwamnan ya zabi wadanda yake so ne kawai.

Kara karanta wannan

ASUU: Ngige ya Zuga Muguwar Karya, Babu Taron Da Aka Gayyacemu Ranar Alhamis

Ya kara da cewa, jam'iyyar APC a jihar karkashin shugabancin Bagudu bata yi wani abu da za ta janyo hankalin masu zabe ba shekarar 2023.

"Sanatan yana matukar biyayya ga shugaban kasa kuma yana yi ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, akasin gwamnan wanda ta kanshi kawai yake yi.
"Baya mutunta su. Wadannan su ne jama'ar da suka kai shi inda yake. Tun daga PDP shma zo suka saka shi takara a 2014 kuma yaci zabe.
"Su ne wadanda suka zuba duk wasu abubuwan da ake bukata domin tabbatar da ya zama gwamna, amma a yau ya mayar dasu makiyansa," Muhammad yace.

Yace gwamnan yafi kwashe lokaci a Abuja fiye da jihar Kebbi inda ya dace ya hidimtawa wadanda suka zabe shi.

Kebbi da Wasu Jihohi 3 da FG ta Gwangwaje da $322m na Kudin Da Abcaha Ya Wawura

A wani labari na daban, an kara jihohi hudu na Edo, Ondo, Enugu da Kebbi cikin wadanda zasu amfana daga $322.5 miliyan na kudin da marigayi shugaban kasa, Janar Abacha ya sace.

Kara karanta wannan

Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani

Daily Trust ta ruwaito cewa, Daraktan ANEEJ, Rabaran David Ugokor, ya bayyana hakan jiya yayin ganawa da manema labarai game da kokarin da kungiyar take wajen lura da sakin kudin.

Al'ummar 'yan kasa na daya daga cikin wadanda suka amince da alhakin sarrafa kudin da aka gano a Switzerland daga wani kaso na NASSP wanda za a raba wa talakawa da marasa karfi na Najeriya, wanda yana daya daga cikin tsarin magance talauci na National Social Investment Programme.

Asali: Legit.ng

Online view pixel