Yadda aka hallaka mutane 3478, aka yi garkuwa da Bayin Allah 2256 a watanni 6

Yadda aka hallaka mutane 3478, aka yi garkuwa da Bayin Allah 2256 a watanni 6

  • Lissafin Nigeria Security Tracker ya nuna an rasa mutum kusan 3500 a cikin kwanaki 195 a Najeriya
  • Alkaluman Nigeria Security Tracker na nufin a kowace rana, sai mutum 17 sun bakunci barzahu
  • Baya ga kashe mutane babu gaira babu dalili, daga Disamban bara zuwa yanzu, an dauke mutum 2200

Nigeria - Akalla mutane 3, 478 aka tabbatar da mutuwarsu, a daidai lokacin da aka yi garkuwa da wasu mutane 2, 256 a cikin watanni shida a Najeriya.

Jaridar 21st Century Chronicle ta ce Nigeria Security Tracker da ke karkashin majalisar huldar kasa da kasa na Amurka ya fitar da wadannan alkaluma.

Wadannan kashe-kashe da satar mutane sun faru daga Disamban 2021 zuwa 15 ga watan Yunin 2022.

Wadanda suka yi wannan kashe-kashe ba kowa ba ne illa miyagun ‘yan bindiga, ‘yan ta’dda, ‘yan bindiga dadi, ‘yan fashi da makami da ma jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

Idan aka bi abin wata-wata, Punch ta ce a Disamban 2021 da aka fara lissafi, mutane 342 aka kashe ba tare da wani dalili ba, aka kuma sace mutum har 397.

Disamban 2021 zuwa Yunin 2022

A watan Junairun bana, ana da lissafin hallaka mutane 603, a daidai lokacin da aka yi garkuwa da wasu da-dama. Abin ya fi yin kamari a Zamfara da Neja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugabannin tsaro
Shugabannin tsaro na kasa Hoto: @BashAhmad
Asali: Facebook

Alkaluman watan Fubrairu sun tabbatar da mutuwar Bayin Allah kusan 500. Baya ga haka, akwai sama da mutane 320 da suka fada hannun masu garkuwa.

Ta'adin ya gawurta sosai a watan Maris da abin ya shafi mutane sama da 1000. ‘Yan bindiga sun kashe mutane 606, sannan an dauke 450 domin karbar fansa.

A watan Afrilu kuwa, rahoton ya tabbatar da cewa an kashe rayuka 530, an dauke 79. Wadanda aka sace a Mayu sun kai 170, aka kuma hallaka wasu 395.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

Mutane 266 aka kashe a cikin makonni biyu da aka yi a watan Yunin nan, an kuma dauke 223.

Ta'adi a kowane yanki

Wadannan ‘yan bindiga da suka hana al’umma sakat sun fi yin ta’adi a Arewa maso tsakiya, Arewa maso yamma da yankin Arewa maso gabashin kasar.

A Kudu maso yamma da Kudu maso gabas, ana fama da matsalar makiyaya da ‘yan kungiyar asiri, A Kudu maso gabas, ‘Yan IPOB ne ke ta hallaka jama’a.

Abdussalami Abubakar ya warke

Ku na da labari cewa Janar Abdussalami Abubakar ya bayyana asalin abin da ya faru da shi, har aka sheka da shi zuwa kasar waje, ya ce yanzu ya dawo garau.

Tsohon shugaban kasar na mulkin soja ya zo bai iya tafiya a lokacin da ake shirin taya shi murnar cika shekara 80. Hakan ta sa ya je ganin Likitoci a Birtaniya.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

Asali: Legit.ng

Online view pixel