Bayelsa: Fusatattun Matasa Sun Kona Wani Da Ake Zargi Da Sata

Bayelsa: Fusatattun Matasa Sun Kona Wani Da Ake Zargi Da Sata

  • Fusatattun matasa sun hallaka wani matashi da ake zarginsa da aikata sata a Yenagoa, Jihar Bayelsa
  • Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ana zarginsa ne da sace wa wani waya mai tsada tare da abokansa su uku
  • Ganau din ya kara da cewa wanda ake zargin yana rike da bindiga AK-47 amma matasan suka kwace sannan suka saka masa taya a wuya suka kona shi

Yenagoa, Bayelsa - Wasu fusatattun matasa, a ranar Asabar sun kona wani da ake zargin barawo ne a Bayelsa, babban birnin jihar.

Lamarin ya faru ne a kusa da Customs Road Junction a Biogbolo-Epie kusa da babban titin Isaac Boro kamar yadda The Punch ta rahoto.

Taswirar Jihar Bayelsa.
Bayelsa: Fusatattun Matasa Sun Kona Wani Da Ake Zargi Da Sata. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Shagon Askin Da Mata Ke Wa Maza Rawa da Tausa, Tace Ba Kai Kadai Suke Askewa Ba

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wanda ake zargin, da ba a iya tabbatar da sunansa ba, an ce an kama shi ne wai yana sace wani waya mai tsada daga hannun wani.

An tattaro cewa matashin mai hasken fata, ya kai shekaru 30, kuma yana cikin wata tawaga da suka kware wurin amfani da adaidaita sahu wurin yi wa mutane fashi.

Amma, sauran yan tawagar biyu sun tsere yayin da shi kuma mutane suka kama shi, bayan wani da suka yi wa satar ya gansu ya gane su.

A lokacin da wakilin The Punch ya isa wurin, ya tarar hayaki na tashi daga abin da ya yi saura na jikin wanda ake zargin, da aka kona da tayar mota.

Ganau sun yi bayanin abin da ya faru

Wasu da abin ya faru a gabansu sun ce yana rike da bindiga AK-47 lokacin da fusatattun matasan suka tasar masa, suka kwace bindigan kuma suka rataya masa taya a wuya, suka cinna masa wuta da fetur.

Kara karanta wannan

Na gazawa mutanena: Gwamnan Ondo ya fashe da kuka wiwi yayin binne wadanda harin coci ya ritsa da su

Daya cikinsu ya ce:

"Ya sace wayar salula mai tsada ne. Su uku ne a Keken. Yana rike da AK-47, sauran biyun sun tsere amma an kama shi.
"Mutane sun amshe bindigan daga hannunsa suka kawo taya suka saka masa a wuya sannan aka cinna wuta. Na ji wai budurwarsa ta zo nan, ta ce ta masa gargadi kada ya tafi wurin satar. Mutanen sun kira yan sanda bayan sun cinna masa wuta."

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan ta'adda sun harba bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel