Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari na jagorantar zaman shawo kan matsalar tsaro

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari na jagorantar zaman shawo kan matsalar tsaro

  • Yanzun nan muke samun labarin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taro da tawagar tsaron Najeriya
  • Ana kyautata zaton tawagar za ta tattauna da Buhari ne kan habaka hanyoyin ragargazar makiya kasar
  • Najeriya dai na fuskantar matsalolin tsaro da dama, kama daga yankin Arewa har zuwa Kudancin kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaron kasar nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja, The Nation ta ruwaito.

Ana sa ran taron zai tattauna batutuwan da suka shafi dabarun bunkasa nasarorin da aka samu a baya-bayan nan wajen yaki da ta'addanci da rashin tsaro gaba daya.

Buhari na jagorantar taron tsaro a fadarsa
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari na jagorantar zaman shawo kan matsalar tsaro | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha da Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 6 da suka marawa Yemi Osinbajo baya akan Bola Tinubu

A gefe guda akwai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojoji, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao suma sun halarci taron.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa'i Abubakar.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel